Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wani matashi mai shekaru 30, Pere Odese, ya kashe mahaifinsa, Friday Odese, yayin da saɓani ya ɓarke a tsakaninsu kan abinci a Jihar Edo.
Lamarin ya faru ne a ƙauyen Ikhehe, Ewato, a ƙaramar Hukumar Esan ta Kudu Maso Yamma ta jihar.
Rahotanni sun ce rikicin ya samo asali ne lokacin da mahaifin ya shaida wa ɗansa cewa babu abinci a gidan.
Mahaifin ya kuma bayyana cewa bai samu damar zuwa gonarsa ba saboda matsalar tsaro da kuma barazanar ’yan bindiga a yankin.
Wannan ya jawo faɗa a tsakaninsu.
A lokacin rikicin, an ce ɗan ya ɗauki adda ya farmaki mahaifinsa, inda ya kashe shi har lahira.
Wani mazaunin yankin ya ce wani maƙwabcinsu da ya yi ƙoƙarin shiga tsakani ya samu rauni, amma yana asibiti inda yake jinya.
Bayan haka, matashin ya yi ƙoƙarin tserewa, amma jama’ar yankin suka bi shi sun kama shi, sannan suka yi masa dukan kawo wuƙa wanda ya yi sanadin mutuwarsa.
Hakan dai ya yi sanadin mutuwar ɗa da mahaifi.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Edo, ta ce tana da masaniya kan abin da ya faru, amma har yanzu ba a kai mata rahoton lamarin a hukumance ba.
