EFCC ta gurfanar da wani bisa zargin yi wa hukumar sojan gona 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta gurfanar da wani mutum mai suna Salifu Olije Mustapha a gaban Kotun Babban Birnin Tarayya da ke Kubwa, bisa zargin yin ƙarya da bayyana kansa a matsayin jami’in hukumar.

A cewar sanarwar da kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya fitar, an gurfanar da wanda ake zargin ne kan tuhume-tuhume guda huɗu da suka haɗa da yin sojan gona da kuma yaudarar jama’a.

ɗaya daga cikin tuhume-tuhumen ya bayyana cewa Mustapha ya yi ƙaryar kasancewa jami’in Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya, sannan ya taimaka wa wasu mutane biyu wajen sanya kayan aikin EFCC tare da amfani da motar Toyota Corolla domin damfarar jama’a a yankin Wuse II da ke Abuja.

Haka kuma, an zarge shi da amfani da sunan jami’in gwamnati wajen damfarar mutane masu yawa.

Bayan karanta masa tuhume-tuhumen, Mustapha ya amsa laifinsa, lamarin da ya sa lauyan masu gabatar da ƙara, R.U Adaga, ya roƙi kotu ta yanke masa hukunci.

Mai shari’a A.I. Akobi ta ɗage shari’ar zuwa ranar 1 ga Yuni, 2026 domin yanke hukunci.

Rahotanni sun ce jami’an EFCC sun kama Mustapha ne bayan samun bayanan sirri da suka alaƙanta shi da sanya kayan bogi na EFCC tare da tsoratar da masu ababen hawa da karɓar kuɗi daga hannunsu.

By ukarofi