Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta tabbatar da kama wata mata da ake zargi da kashe uwargidan mijinsu bayan ta soka mata wuƙa har lahira a unguwar Gwargwaje da ke Zariya.
Kakakin rundunar, DSP Mansir Hassan, ya ce lamarin ya faru ne a Unguwar Madachi B da ke yankin Gwargwaje, inda ake zargin wata mata mai suna Amina ta kai wa uwargidanta, Amina Maharazu, hari da wuƙa.
Ya ce bayan samun rahoton faruwar lamarin daga mai unguwa, jami’an ’yan sanda sun garzaya wurin, inda suka tarar da matar kwance cikin jini tana cikin mawuyacin hali.
“An yi ƙoƙarin kai ta asibiti domin ceto rayuwarta, amma ta rasu kafin a kai ta,” inji kakakin.
DSP Hassan ya ce an kama wadda ake zargi kuma an miƙa ta zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka (SCID) domin ci gaba da bincike kafin gurfanar da ita a gaban kotu.
Ya ƙara da cewa Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kaduna ya yaba wa jami’an yankin Dan Magaji bisa yadda suka gaggauta ɗaukar mataki bayan samun rahoton aukuwar lamarin.
Da yake magana kan abin da ya faru, mijin matan, Salisu Haruna, ya ce marigayiyar ce ta taimaka wajen haɗa aurensa da amaryar da ake zargi, inda cikin alhini, ya ce bai taɓa tsammanin za a kai ga wannan mummunan ƙarshe ba.
A nasa ɓangaren, Mai Unguwar Madachi B, Yamusa Sani Sarkin Fada, ya ce an sanar da shi faruwar lamarin ne da misalin ƙarfe 11:30 na dare a ranar 30 ga watan Mayu.
“An kira ni aka ce matan gidan suna faɗa, kuma an soka wa uwargida wuƙa. Nan take na sanar da DPO na Dan Magaji domin ɗaukar matakin gaggawa,” inji shi.
Wasu maƙwabta sun shaida wa Aminiya cewa rikicin ya samo asali ne daga saɓani kan rabon naman Sallah, inda ake zargin amaryar ta yi fusata ne bayan ta yi zargin cewa an fifita ’ya’yan uwargidan akan ɗanta wajen rabon naman.
Majiyoyin sun ce tun kafin wannan lokaci ana samun saɓani a gidan, musamman idan yara suka samu saɓani, amma sun bayyana marigayiyar a matsayin mace mai haƙuri da son zaman lafiya.
Marigayiyar ta shafe shekaru da dama tare da mijinta, kuma ta bar ’ya’ya takwas da jikoki, yayin da aka ruwaito cewa ta riga ta aurar da biyu daga cikin ’ya’yanta.
.
