Sanannen basaraken Nijeriya ya rasu a Misra

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Masarautar Ngazargamu ta sanar da rasuwar sarkinta Mai Martaba Mai Ngazargamu Alhaji Tijjani ibn Saleh Geidam.

Marigayin ya rasu ne a ranar Talata, 9 ga watan Yuni, 2026 a Misra bayan tsawon lokaci yana jinyar rashin lafiya, kamar yadda wata sanarwa daga masarautar ta bayyana.

Za a kawo gawar marigayin zuwa Nijeriya domin yi masa jana’iza a Damaturu, inda masarautar ta ce za a sanar da rana lokaci daga bisani.

Alhaji Muhammad Alamai Baba Kankare, wanda ya sanya wa sanarwar hannu kuma Wazirin masarautar, ya roƙi jama’ar Musulmi da su sanya marigayin a addu’o’insu na samun rahamar Allah.

By Babaji

Leave a Reply