
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Talata Shugaba Bola Tinubu ya ƙaddamar da manyan ayyuka tattali da ababen more rayuwa a garin Ado-Ekiti, Babban Birnin Ekiti, a wata ziyarar aiki ta kwana biyu a jihar.
Daga cikin ababen da aka ƙaddamar akwai sabon ofishin reshe na Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) akan hanyar Old Iyin a Ado-Ekiti da kuma kilomita 1.2 na babbar gada da aka yi wa laƙabi da Okeyinmi, a matsayin gagarumar nasara a fagen ababen more rayuwa da za fa sauƙaƙe lamuran zirga-zirga a birnin.
Kakakin mataimakin shugaban ƙasa, Stanley Nkwocha ya bayyana haka a wata takarda da ya fitar a ranar Talata.
Tinubu, wanda mataimakinsa, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya wakilce shi, ya kuma ƙaddamar da cibiyar ilimi ta EKZ da nufin inganta amfani da fasaha, ƙirƙira da ci-gaban tattali a mai dogon zango a jihar.
Da yake jawabi yayin ƙaddamar da cibiyar, Shugaba Tinubu ya ce rashawa ba zai samu gindin zama ba a gwamnatinsa, yana mai tabbatar da ƙoƙarin gwamnatin na ƙarfafa cibiyoyin yaƙi da ita da tabbatar da gaskiya da adalci a ma’aikatun gwamnatin da na ɗaiɗaikun mutane a Nijeriya.
Ya kuma gargaɗi jami’ai masu hannu a laifukan rashawa da cewa gwamnatinsa za ta yaƙi al’amarin ba tare da gajiyawa ba, yana mai bayyana EFCC a matsayin hukumar samar da dabarun zuba jari wajen inganta cibiyoyi, yardar al’umma da kuma ci-gaban ƙasa.
A cewarsa, ɗorewar nasarori da ci-gaban Nijeriya ya dogara ne da sahihancin ma’aikatun gwamnati, inda ya yi gargaɗin hakan ba zai yiwu ba yayin da rashawa ke cigaba da lalata dangantakar da ke tsakanin ‘yan ƙasa da ƙasar.



