Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina
Majalisar zartarwa ta amince da samar da fitulu masu amfani da hasken rana guda talatin talatin da ke gundumomi 361 domin rabawa a makaratun Allo da ke faɗin jihar.
A zaman ta karo na tara ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar malam Dikko Raɗɗa majalisar ta kuma amince da matakai na inganta rayuwar al’umma.
Muhimman abubuwan da majalisar ta amince da su kamar yadda kwamishinan yaɗa labarai Dr Salisu Bala Zango ya shaidawa manema labarai a Katsina sauran sun haɗa da samar da rumfunar kasuwanci na zamani guda 2000 a ƙarƙashin shirin haɓaka ƙananan masana’antu da ke kan manyan titunan a ƙarƙashin hukumar KASEDA.
Haka kuma majalisar zartarwa ta jihar ta amince da aiwatar da tsarin bibiyar kasafin kuɗin jihar don ya yi daidai da tsarin da zai rage sauyin yanayi a dukkan ma’aikatu da hukumomin gwamnati da kuma ƙananan hukumomin jihar.
Ta amince da aiwatar da tsarin bibiyar kasafin kuɗin jihar don ya yi daidai da tsarin da zai rage Sauyin yanayi (Climate Change Budget Tagging) a dukkan ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnati (MDAs), da kuma ƙananan hukumomin jihar.
Wannan mataki a cewar kwamishinan zai inganta tsare-tsare da kashe kuɗaɗen ayyukan da suka shafi sauyin yanayi, tare da ƙarfafa ci gaba mai ɗorewa, kare muhalli, da bunƙasa tattalin arzikin Jihar Katsina.
