‘Yadda Ibo suka mallake gidajen Legas suka maida Yarabawa ’yan haya’

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Fitaccen mawaƙin Nijeriya, Tobechukwu Melɓin Ejiofor, wanda aka fi sani da IllBliss, ya shiga tsaka mai wuya a kafafen sada zumunta bayan wata muhawara mai zafi da ta shafi zuba jari da mallakar filaye da al’ummar Ibo ke yi a Jihar Legas.

Cece-kucen ya fara ne bayan da mawaƙin ya wallafa saƙo a shafinsa na ɗ (wanda aka fi sani da Twitter a baya), inda ya kare gudunmawar da al’ummar Ibo suka bayar ga tattalin arzikin Legas.

A cewarsa, al’ummar Ibo sun taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa harkokin kasuwanci da kuma fannin gidaje a jihar.

“’Yan Ibo sun bayar da gagarumar gudunmawa ga tattalin arzikin Legas ta fuskar kasuwanci. Idan wani yana da matsala da hakan, ya rungumi tiransifoma. Mun zuba jari mai yawa a harkar gidaje. Sauran ƙabilu ma sun bayar da gudunmawa. Me ya sa idan Ibo ne kawai ake mayar da abin matsala?” inji shi.

Kalaman nasa sun haifar da martani daga masu amfani da kafar, ciki har da wani mai suna @IgeOlusayo47761, wanda ya buƙace shi da ya mutunta Legas tare da nuna godiya ga damar da jihar ta ba shi da sauran ’yan kasuwa.

Sai dai rahotanni sun ce muhawarar ta ƙara ɗaukar zafi bayan wani saƙo da ake zargin IllBliss ya wallafa — wanda daga baya aka ce an goge shi — ya bayyana a yanar gizo.

A cikin saƙon da ake zargin ya wallafa, mawaƙin ya yi iƙirarin cewa ’yan Ibo sun mallaki manyan filaye a Legas, kuma suna sake ba ’yan asalin jihar haya.

Rahoton ya ce: “Mun mallaki filayenku. Mun sayi wurare da dama kuma muna sake ba ku haya. Na gode Legas saboda damar da ta ba mu. Za ku ci gaba da biyan haya har abada a wannan birni.”

Sai dai babu wata hujja mai zaman kanta da ta tabbatar da sahihancin wannan saƙo.

Bayan yaɗuwar iƙirarin, masu amfani da kafafen sada zumunta da dama sun bayyana rashin jin daɗinsu, suna masu cewa irin waɗannan kalamai na iya ƙara rura wutar rikicin ƙabilanci tsakanin ’yan asalin Legas da al’ummar Igbo.

Wasu masu sharhi sun yi gargadin cewa irin waɗannan maganganu na iya janyo ƙiyayya da rashin fahimta, musamman idan aka yi la’akari da yadda rikice-rikicen ƙabilanci suka taɓa tasowa a wasu ƙasashen Afirka.

Wasu kuma sun jaddada cewa duk wanda ya samu damar zama ko kasuwanci a wata al’umma ya kamata ya nuna ladabi da girmamawa ga mazauna yankin.

Lamarin ya ɗauki wani sabon salo bayan da wasu masu amfani da yanar gizo suka sake yaɗa wani tsohon bidiyon tattaunawar IllBliss, inda ya taɓa magana kan nuna wariya tsakanin wasu al’ummomin Ibo.

A cikin bidiyon, mawakin ya yi zargin cewa a wasu lokuta ana fifita mutane bisa jiha, ƙaramar hukuma ko yankin da suka fito a Kudu maso Gabashin Nijeriya.

Wasu masu sukar sa sun yi amfani da wannan bidiyo wajen zargin mawakin da nuna saɓani a kalamansa, suna cewa a baya ya soki irin wannan wariya, amma yanzu shi ne ya shiga cikin wata magana da ta tayar da ƙura.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, IllBliss ko wakilansa ba su fitar da wata sanarwa a hukumance domin tabbatarwa ko ƙaryata kalaman da ake danganta masa ba.

By ukarofi

Leave a Reply