Abdulsamad ba shi da alaƙa da bidiyon zuba jarin da ke yawo a intanet – BUA

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kamfanin BUA ya nesanta kansa daga wani bidiyo da aka ƙirƙira ta hanyar ƙirƙirarriyar Basira ra AI wanda ke yawo a kafafen sada zumunta, inda aka yi amfani da hoton wanda ya kafa kuma Shugaban Kamfanin, Alhaji Abdulsamad Rabiu, wajen tallata wani shirin zuba jari da kamfanin ya ce na yaudara ne.

A cikin wata sanarwa da kamfanin ya wallafa a shafukansa na hukuma ranar Litinin, BUA ya bayyana cewa bidiyon na ɗauke da alƙawuran samun riba mai yawa cikin gaggawa, kuma an ƙirƙire shi ne domin yaudarar jama’a tare da jawo su shiga wani shiri da ba shi da tushe.

Kamfanin ya jaddada cewa babu wata alaƙa tsakaninsa da wannan dandali ko kuma duk wata da’awar da ake yi a cikin bidiyon.

Sanarwar ta ce, “Ko Shugaban Kamfaninmu, Alhaji Abdulsamad Rabiu, ko BUA, ko kuma wani kamfani da ke ƙarƙashinsa, ba su da wata alaƙa ko haɗin gwiwa da wannan dandali ko kuma alƙawuran saka hannun jarin da yake tallatawa.”

BUA ya ƙara da cewa, an tsara bidiyon ne da gangan domin a yaudari mutane su ɗauka cewa kamfanin da wanda ya kafa shi sun amince da shirin zuba jarin da ake tallatawa.

Saboda haka, kamfanin ya buƙaci jama’a su yi watsi gaba ɗaya da bidiyon, tare da kauce wa duk wata hulɗa da mutanen da ke tallata irin waɗannan shirye-shiryen da ke alƙawarin samun riba mai yawa cikin ɗan lokaci.

Haka kuma, BUA ta shawarci jama’a da su kai rahoton duk wani abu makamancin haka ga jami’an tsaro domin ɗaukar matakin da ya dace.

Kamfanin ya bayyana cewa wannan lamari wani ɓangare ne na sabon salo na damfara da masu yaudara ke amfani da shi ta hanyar fasahar AI, inda suke kwaikwayon fitattun mutane da manyan kamfanoni domin samun amincewar jama’a da kuma jefa su cikin zamba.

Kamfanin BUA ya sake nanata cewa ba ta da wata alaƙa da dandalin da ake magana a kai, tare da kira ga jama’a da su kasance cikin shiri da taka-tsantsan kan sabbin dabarun damfara da ake aiwatarwa ta hanyar fasahar zamani.

By ukarofi

Leave a Reply