Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kamfanin Mai na Nijeriya (NNPCL) yana fuskantar ƙarin matsin lamba bayan bayanan da suka bayyana cewa, an kashe kimanin Naira biliyan 5.9 wajen yi masa rajista, sauyin tsari da kuma sake fasalin kamfanin daga tsohon Kamfanin Man Fetur na ƙasa (NNPC) zuwa Kamfanin Mai na ƙasa na Nijeriya Mai Zaman Kansa (NNPCL) a ƙarƙashin tanade-tanaden Dokar Masana’antar Man Fetur (PIA).
Abin da aka yi niyya ya zama wata sabuwar alama ta gudanar da harkokin kasuwanci da kyakkyawan tsarin shugabanci a kamfanin mai na ƙasa, ya rikiɗe zuwa wata gagarumar muhawara da ta haifar da fushin jama’a, binciken ’yan majalisa, shigar da ƙara a kotu da kuma kiraye-kirayen neman cikakken bayani kan yadda aka kashe kuɗaɗen.
Masu suka sun yi tambaya kan ko akwai wata hujja mai ƙarfi da za ta tabbatar da kashe irin wannan adadi domin abin da da yawa ke ganin bai wuce sauya suna da tambarin kamfani ba. A lokaci guda, ’yan majalisa da ƙungiyoyin farar hula na neman a fito fili a bayyana yadda aka kashe kuɗin.
Lamarin ya ƙara ɗaukar zafi ne bayan da Kwamitin Majalisar Dattawa Kan Binciken Kuɗaɗen Jama’a ya kalubalanci kuɗin a wani zaman sauraron jama’a kan bayanan kuɗaɗen NNPCL.
Shugaban kwamitin, Sanata Aliyu Wadada Ahmed, ya nuna mamakinsa kan yadda aka kashe Naira biliyan 5.9 wajen rajista da sake fasalin kamfanin, yana mai bayyana adadin a matsayin abin da ke da wahalar fahimta.
Takardun da kwamitin ya bincika sun nuna cewa an raba kuɗin zuwa kashi biyu na kusan naira biliyan 2.95 kowanne. Rahotanni sun ce an ciro wani ɓangare daga kuɗaɗen tallace-tallacen kayayyakin man fetur a matsayin kuɗin rajista, yayin da aka sake ɗora wani adadin iri ɗaya a kan kuɗaɗen danyen mai ta hannun Hukumar Kula da Zuba Jarin Man Fetur ta ƙasa (NAPIMS) domin wannan aiki guda ɗaya.
Kwamitin ya nuna damuwa kan yiwuwar maimaita caji daga mabambantan hanyoyin samun kuɗaɗe domin aiki guda, lamarin da ya haifar da tambayoyi kan gaskiya da riƙon amana.
“Ta yaya za a kashe irin wannan maƙudan kuɗi kawai domin sauya suna daga NNPC zuwa NNPCL a wannan zamani?” Sanata Wadada ya tambaya yayin zaman.
Baya ga kuɗin sake fasalin kamfanin, ’yan majalisar sun kuma nuna damuwa kan wasu bayanan kuɗaɗe da suka kai kusan naira tiriliyan 210 da ke cikin kundin kuɗaɗen kamfanin.
Kwamitin ya ce akwai wasu bayanai guda biyu na naira tiriliyan 103 da kuma naira tiriliyan 107 da har yanzu jami’an NNPCL ba su yi cikakken bayani a kansu ba.
A cewar kwamitin, irin waɗannan adadi ba za a iya kawar da su ta hanyar lissafi kawai ba tare da gabatar da hujjoji da bayanan da suka dace ba.
Sanata Wadada ya ce idan ba a bayar da gamsassun bayanai ba, za a iya buƙatar NNPCL ta yi bayanin kuɗaɗen ko ma ta mayar da su.
Sakamakon haka, Majalisar Dattawa ta gayyaci wasu tsofaffi da na yanzu daga cikin jami’an kamfanin domin su yi bayani kan kuɗin sake fasalin da kuma sauran bayanan kuɗaɗen da ake takaddama a kansu.
Yayin da binciken majalisar ke ci gaba, lamarin ya kuma isa kotu.
ƙungiyar Kare Haƙƙoƙin Tattalin Arziki da Bayar da Lissafi (SERAP) ta shigar da ƙara a kan NNPCL, tana zargin kamfanin da kasa yin cikakken bayani kan yadda aka kashe naira biliyan 5.9.
A ƙarar da aka shigar a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, mai lamba FHC/ABJ/CS/1248/2026, SERAP na neman umarnin kotu da zai tilasta wa NNPCL bayyana dukkan bayanan kuɗin.
ƙungiyar na neman a gabatar da cikakken bayanin yadda aka kashe kuɗaɗen, sunayen kamfanonin da suka yi aikin, irin ayyukan da suka gudanar da kuma yadda aka amince da kashe kuɗin.
Haka kuma SERAP na neman a bayyana sunaye da muƙaman jami’an gwamnati da suka amince da sakin kuɗaɗen, tare da hujjojin da ke nuna an bi dokokin saye da samar da kayayyaki da kuma ƙa’idojin gudanar da gwamnati.
Mataimakin Daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare, ya ce jama’a na da cikakken haƙƙin sanin yadda aka kashe kuɗaɗen jama’a.
“NNPCL na da alhakin bayyana ko wannan kashe kuɗi ya samar da ƙima ga jama’a, ko ya dace da doka da kuma ko an bi ƙa’idojin da suka dace,” inji ƙungiyar.
SERAP ta ƙara da cewa bayyana waɗannan bayanai zai taimaka wa ’yan Nijeriya wajen tantance ko an kashe kuɗin yadda ya kamata da kuma ko an samu darajar abin da aka kashe.
A nasa ɓangaren, masanin harkokin mai da iskar gas, Dakta Samuel Onadi, ya soki adadin kuɗin da aka ruwaito, yana mai kira da a gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa kan lamarin.
Ya ce, duk da cewa sake fasalin kamfanoni abu ne da aka saba yi a hukumomin gwamnati da masu zaman kansu, adadin da aka kashe ya haifar da tambayoyi masu muhimmanci da suka cancanci amsa.
A cewarsa, ’yan Nijeriya ba wai suna son sanin jimillar kuɗin da aka kashe kaɗai ba ne, suna kuma son sanin ayyukan da aka biya wa kuɗin, waɗanda suka yi su da kuma ko an bi hanyoyin da doka ta tanada.
Ya jaddada cewa idan ana son ƙarfafa amincewar jama’a ga hukumomi, dole ne a rungumi gaskiya da riƙon amana.
Dakta Onadi ya kuma bayyana cewa duk da manufar Dokar Masana’antar Man Fetur (PIA) ta mayar da NNPCL kamfani mai cin gashin kansa ta fuskar kasuwanci, dole ne hakan ya zo tare da matakan bayyana gaskiya da za su iya jure binciken jama’a.
Ga masu sa ido da dama, batun kuɗin naira biliyan 5.9 ya wuce cece-kuce kan kuɗin sauya suna kawai. Ya zama gwajin yadda ake tafiyar da al’amuran gwamnati, nuna gaskiya da kuma gina amincewa tsakanin gwamnati da ’yan ƙasa.
Yayin da binciken Majalisar Dattawa ke ci gaba kuma kotu ke shirin sauraron ƙarar SERAP, hankulan jama’a na ci gaba da karkata kan NNPCL.
Sakamakon waɗannan matakai na iya tantance ba kawai ko an kashe kuɗin bisa hujja ba, har ma ko kamfanin zai iya tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa sauyinsa zuwa kamfani mai zaman kansa ya zo da sabon zamani na gaskiya, riƙon amana da nagartaccen shugabanci.
