An dakatar da shugaban APC na Kebbi da na ƙaramar hukumar Zuru

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Jam’iyyar APC reshen Jihar Kebbi ta sanar da dakatar da Alhaji Abubakar Muhammad Kana-Zuru shugaban Jam’iyyar APC na jihar da kuma Honarabul Aliyu Abubakar Abiola shugaban Jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Zuru bisa zarge-zargen karya dokokin jam’iyya da rashin gudanar da ayyukan jam’iyya yadda ya kamata.
Wannan yana ƙunshe ne a cikin wata takarda mai ɗauke da sa hannun Sakataren jam’iyyar na jihar, Alhaji Sa’idu Muhammad Kimba ranar Larabar nan. Takardar ta bayyana cewa matakin ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafe daga masu ruwa da tsaki a yankin masarautar Zuru. Ƙorafe-ƙorafen sun haɗa da rashin himma wajen gudanar da harkokin jam’iyya, rashin tuntuɓar manyan masu ruwa da tsaki, ƙarancin aikin wayar da kan jama’a da kuma rashin bin ƙa’idoji da tsare-tsaren APC.
Bayan binciken cikin gida da jam’iyyar ta gudanar, an yanke shawarar dakatar da shugabannin biyu har sai an kammala bincike wanda shi ne zai tabbatar da irin hukuncin da ya dace kan su.

Wata mai kama da wannan, wata takarda mai ɗauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar Alhaji Yakubu Bala-Tafida, ta shelanta dakatar da kwamishinan raya kiwon dabbobi da kifi na jihar, Alhaji Kabir Usman Alaramma Zuru, daga aiki nan take har sai an sake bayar da wata sanarwa tare da umartar sa da ya gaggauta miƙa duk ƙadarorin gwamnati da ke hannun sa ga babban sakataren ma’aikatar kai tsaye.
Waɗansu majiyoyi daga yankin na zuru sun alaƙanta wannan korar da aka yi wa mutanen da handama da baba-kere da kuma rub-da-ciki da waɗansu kaya na al’umma lokacin zaɓen cike girbin ɗan majalisar jiha bayan rasuwar kakakin majalisar Honarabul Ankwai.

By ukarofi