
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sake tabbatar da aniyar gwamnatinsa na ci gaba da bai wa jami’an tsaro cikakken goyon baya domin ƙarfafa yaƙi da matsalolin tsaro a faɗin jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da ya jagoranci taron mako-mako na Majalisar Tsaro ta Jihar Zamfara da aka gudanar a Fadar Gwamnati da ke Gusau.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, an bayyana cewa taron ya haɗa shugabannin dukkannin hukumomin tsaro da ke aiki a jihar.
Sanarwar ta ce, mahalarta taron sun tattauna hanyoyin ƙara ƙarfafa ayyukan tsaro, musamman a yankunan da ke fama da matsalolin rashin zaman lafiya.
“Gwamna Dauda Lawal ya jagoranci taron mako-mako na Majalisar Tsaro tare da sabunta ƙudirinsa na ƙara tallafa wa jami’an tsaro da ke aiki a jihar,” inji sanarwar.
Ta ƙara da cewa, gwamnan ya tabbatar wa shugabannin hukumomin tsaro cewa gwamnatinsa za ta ɗauki duk matakan da suka dace domin inganta walwala da yanayin aikin jami’an da ke fafutukar tabbatar da tsaro a Zamfara.
A cewar sanarwar, taron ya mayar da hankali kan muhimman batutuwa da suka haɗa da ƙara yawan jami’an tsaro a yankunan da ke fuskantar barazana, da kuma inganta saurin kai ɗauki yayin aukuwar lamurran gaggawa.
Gwamna Lawal ya jaddada cewa babban burinsa shi ne ganin an samu cikakken tsaro da zaman lafiya a Zamfara, yana mai tabbatar wa shugabannin hukumomin tsaro cewa ƙofar ofishinsa a buɗe take domin tattauna duk wata matsala ko buƙatar da za ta taimaka wajen cimma wannan manufa.
Ya kuma nuna cewa haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da hukumomin tsaro na da matuƙar muhimmanci wajen magance ƙalubalen tsaron da jihar ke fuskanta.



