Jam’iyyun adawa sun yi watsi da sakamakon zaɓen Gwamnan Ekiti

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Jam’iyyun adawa a Jihar Ekiti sun bayyana rashin amincewarsu da sakamakon zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar, inda suka yi zargin cewa an tafka kura-kurai da kuma sayen ƙuri’u a yayin zaɓen.

A sakamakon da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta sanar, gwamna mai ci, Biodun Abayomi Oyebanji na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya samu nasarar lashe zaɓen tare da sake samun wa’adin mulki na tsawon shekaru huɗu.

Sai dai jam’iyyun adawa da suka haɗa da Peoples Democratic Party (PDP) da African Democratic Congress (ADC) sun nuna rashin gamsuwa da yadda aka gudanar da zaɓen, suna masu cewa akwai zarge-zargen sayen ƙuri’u da wasu abubuwan da suka saɓa wa ƙa’idojin zaɓe.

A wani shirin tattaunawa na Nigeria Daily wanda Daily Trust ta gabatar, wakilan jam’iyyun adawar sun bayyana dalilan da suka sa ba za su amince da sakamakon zaɓen ba, tare da yin nuni da yiwuwar ɗaukar matakan shari’a domin ƙalubalantar sakamakon.

Masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin cewa sakamakon zaɓen Ekiti zai kasance wani muhimmin gwaji ga jam’iyyun siyasa gabanin babban zaɓen shekarar 2027, musamman wajen auna ƙarfin jam’iyyun adawa da kuma tasirin APC a matakin ƙasa.

Yayin da magoya bayan APC ke ci gaba da murnar nasarar Oyebanji, ana sa ran muhawara da ƙorafe-ƙorafen da suka biyo bayan zaɓen za su ci gaba da jan hankalin masu ruwa da tsaki a harkokin dimokuraɗiyya.

Masu lura da al’amuran siyasa na cewa yadda za a warware korafe-korafen da aka gabatar zai taimaka wajen ƙarfafa amincewar jama’a da tsarin zaɓe da kuma tabbatar da sahihancin dimokuraɗiyya a Nijeriya.

By ukarofi

Leave a Reply