Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja kuma jagoran jam’iyyar PDP na ƙasa, Nyesom Wike, ya buƙaci mambobin jam’iyyar su shirya tsaf domin fafatawar siyasa mai zafi da ke tafe gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Wike ya bayyana cewa ba a bayar da mulki kyauta a siyasa, sai an yi gwagwarmaya da jajircewa kafin a samu nasara.
Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin taron Kwamitin Zartarwa na ƙasa (NEC) karo na 109 na jam’iyyar PDP da aka gudanar a Abuja.
A jawabinsa, tsohon gwamnan Jihar Ribas ya yi kira ga ’yan takarar jam’iyyar da kada su ji tsoron kama su da hukumomi ko kuma fuskantar shari’o’i, yana mai cewa nasara a siyasa tana zuwa ne ta hanyar jure ƙalubale da wahalhalu.
“Babu wanda ke ba da mulki. Mulki ana kwace shi ne ta hanyar gwagwarmaya. Ba wanda zai miƙa maka shi a kyauta. Dole ne ka yi ƙoƙari, ka yi fafutuka domin samun sa. Kada ku ji tsoro,” inji shi.
Wike ya kuma jaddada muhimmancin ƙarfafa jam’iyyar daga matakin ƙasa har zuwa karkara, yana mai kira ga mambobi da shugabannin jam’iyyar su tabbatar sun samar da gagarumar gudunmawa kafin zaɓen 2027.
Ya ce kowane ɗan jam’iyya ya kamata ya koma mazabarsa ya yi aiki domin samun wakilai da za su ci zaɓe a matakai daban-daban.
“Idan ka kawo ɗan Majalisar Wakilai, ka yi wani abu. Idan ka kawo ɗan Majalisar Jiha, ka yi wani abu. Amma kada ku zo da hannu wofi, domin wannan ba wurin masu hannu wofi ba ne,” inji ministan.
Ya ƙara da cewa duk wanda ke shiga siyasa dole ne ya kasance a shirye ya fuskanci matsin lamba da ƙalubale, domin hakan wani ɓangare ne na gwagwarmayar siyasa da ke nuna jajircewa da biyayya ga manufar da mutum ya runguma.
Da yake magana kan shirye-shiryen jam’iyyar gabanin zaɓe, Wike ya bayyana cewa PDP na tafiya yadda ya kamata wajen shirye-shiryenta, duk da ƙalubalen da take fuskanta a halin yanzu.
Ya kuma nuna cewa jam’iyyar ba ta damu da batutuwan shari’a da ke gabanta ba, yana mai cewa kotuna an kafa su ne domin mutane su nemi haƙƙoƙinsu.
A cewarsa, duk da matsalolin cikin gida da PDP ke fuskanta, jam’iyyar za ta ci gaba da kasancewa wata muhimmiyar ƙarfi a siyasar Nijeriya.
“Bayan zaɓen 2027, za mu sake dawowa nan mu gode wa Allah da ya raya jam’iyyarmu. Ko da yake a yanzu ba mu cikin matsayin da za mu ce dole ne mu samu komai, amma idan muka kasance adawa mai ƙarfi, za mu ci gaba da zama masu tasiri kuma mu tsara makomarmu,” inji Wike.
Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyun siyasa ke fara tsara dabarunsu domin babban zaɓen 2027, wanda ake sa ran zai kasance ɗaya daga cikin zaɓukan da za su fi zafi a tarihin siyasar Nijeriya.
