Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kungiyar Kare Haƙƙin Bil’Adama ta ƙasa da ƙasa, wato International Human Rights Commission – Relief Fund Trust (IHRC-RFT) Nigeria, ta bayyana matuƙar alhini, damuwa da kuma Allah-wadai kan mummunan kisan gillar da aka yi wa Malama Ummulkhairi a yankin Mararaban Jos da ke ƙaramar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna, bayan wasu mutane sun zarge ta da wani laifi tare da ɗaukar doka a hannunsu ba tare da an gabatar da ita gaban hukumomin da suka dace ko kotu ba.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata Amb. Abdullahi Bakoji Adamu, Daraktan ƙasa na IHRC-RFT ya sanya wa hannu.
Kungiyar ta bayyana lamarin a matsayin babban take haƙƙin ɗan Adam da kuma cin zarafin dokokin ƙasa, tana mai jaddada cewa babu wani mutum ko wata ƙungiya da ke da ikon yanke hukunci ko aiwatar da hukunci kan wani ɗan ƙasa ba tare da bin hanyoyin da doka ta tanada ba.
IHRC-RFT Nigeria ta tunatar da al’umma cewa haƙƙin rayuwa na daga cikin muhimman haƙƙoƙin ɗan Adam da Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Nijeriya da kuma dokokin ƙasa da ƙasa suka tabbatar. Sashe na 33(1) na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Nijeriya na shekarar 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima) ya tanadi cewa kowane ɗan ƙasa yana da haƙƙin rayuwa, kuma ba za a iya hana shi wannan haƙƙi ba sai bisa hukuncin kotu bayan an same shi da laifi kamar yadda doka ta tanada.
Haka kuma, Sashe na 34(1) na kundin tsarin mulkin ya tabbatar da mutuncin ɗan Adam tare da haramta duk wani nau’i na cin zarafi, azabtarwa ko wulaƙanta mutum. Saboda haka, kashe mutum ko ƙona shi da rai ta hanyar hukuncin taron jama’a babban laifi ne kuma ya saɓa wa tanade-tanaden kundin tsarin mulki.
Kungiyar ta kuma yi nuni da cewa Sashe na 36(1) na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya tabbatar da haƙƙin samun shari’a cikin adalci, yayin da Mataki na 10 na UDHR ya tanadi cewa kowane mutum yana da haƙƙin a saurare shi cikin gaskiya da adalci a gaban kotu mai zaman kanta kafin a yanke masa hukunci.
Haka zalika, Mataki na 3 na wannan sanarwar duniya kan haƙƙin ɗan Adam ya bayyana cewa: “Kowane mutum yana da haƙƙin rayuwa, ’yanci da kariya ga lafiyarsa.”
A cewar ƙungiyar, ko da mutum yana fuskantar zargi, hakan ba ya cire masa haƙƙinsa na samun kariyar doka da kuma damar kare kansa a gaban kotu. A tsarin dimokuraɗiyya da bin doka, kotu ce kaɗai ke da ikon tantance laifi da yanke hukunci, ba taron jama’a ba.
IHRC-RFT Nigeria ta nuna damuwa kan yadda zarge-zarge, jita-jita da hasashe ke ci gaba da zama sanadin salwantar rayukan jama’a a wasu sassan ƙasar nan. ƙungiyar ta bayyana cewa ɗaukar doka a hannu na barazana ga zaman lafiya, tsaro da haɗin kan al’umma.
Kungiyar ta yabawa hukumomin tsaro bisa kama wasu da ake zargi da hannu a wannan aika-aika, amma ta bukaci Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya da sauran hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike mai zurfi, gaskiya da adalci domin gano duk wanda ya shirya, ya aiwatar ko ya taimaka wajen aikata wannan ɗanyen aiki.
Har ila yau, ƙungiyar ta yi kira ga hukumomin shari’a da su tabbatar da gurfanar da duk waɗanda bincike ya nuna suna da hannu a lamarin domin su fuskanci hukuncin da doka ta tanada. Ta jaddada cewa dole ne a yi adalci ba tare da la’akari da matsayin mutum, addini, ƙabila ko wata alaƙa ba.
IHRC-RFT Nigeria ta bayyana cewa za ta ci gaba da sanya ido kan yadda binciken wannan lamari ke gudana tare da bibiyar matakan da hukumomi ke ɗauka domin tabbatar da cewa an yi cikakken adalci ga marigayiya Malama Ummulkhairi da iyalanta.
ƙungiyar ta kuma yi kira ga shugabannin addinai, sarakunan gargajiya, ƙungiyoyin farar hula, kafafen yaɗa labarai da sauran al’umma da su ƙara wayar da kan jama’a kan muhimmancin mutunta doka, kare haƙƙin bil’adama da kuma gujewa yanke hukunci bisa jita-jita, hasashe ko zargi.
A cewar ƙungiyar, tabbatar da adalci ga Malama Ummulkhairi ba nauyin iyalanta kaɗai ba ne, alhaki ne da ya rataya a wuyan al’umma baki ɗaya. Rashin hukunta masu hannu a irin wannan mummunan aiki na iya ƙara ƙarfafa masu ɗaukar doka a hannu tare da jefa zaman lafiyar al’umma cikin haɗari.
A ƙarshe, IHRC-RFT Nigeria ta miƙa sakon ta’aziyyarta ga iyalan marigayiyar, ’yan uwanta da dukkan waɗanda wannan mummunan lamari ya shafa. ƙungiyar ta yi addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya jiƙanta da rahama, Ya gafarta mata kura-kuranta, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarta, Ya kuma bai wa iyalanta da masoyanta juriyar wannan babban rashi.
