
Babbar Kotun Jihar Kaduna ta ƙi amincewa da buƙatar beli da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya gabatar, inda ta umarci cewa zai ci gaba da kasancewa a hannun Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) har sai an cigaba da shari’ar.
A hukuncin da Mai Shari’a Dirisu Khobo ya yanke a ranar Litinin, ya bayyana cewa El-Rufai bai gabatar da hujjoji masu gamsarwa da za su sa kotu ta yi amfani da ikon ta wajen ba shi beli ba.
Kotun ta kuma ce babu wasu dalilai na musamman da suka cancanci a sake shi kafin kammala shari’ar. El-Rufai bai halarci zaman kotun lokacin da aka yanke hukuncin ba.
Ana tuhumar tsohon gwamnan da laifuffuka guda tara da suka haɗa da amfani da mukami ba bisa ƙa’ida ba da wasu laifuka masu alaƙa.
Tun farko dai tuhume-tuhumen sun kai guda goma, amma bayan gyaran da masu gabatar da ƙara suka yi, an rage su zuwa tara, kuma El-Rufai ne kaɗai ya rage a matsayin wanda ake tuhuma. Ya musanta dukkan zarge-zargen.
Sai dai duk da ƙin ba shi beli, kotun ta umarci ICPC da ta tabbatar El-Rufai na samun cikakkiyar dama wajen ganin likitocinsa ko kuma zuwa duk wata cibiyar lafiya da ya zaɓa a cikin Najeriya idan bukatar hakan ta taso yayin da yake tsare.
An ɗage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranakun 7 da 8 ga Yuli, 2026, inda ake sa ran masu gabatar da ƙara za su fara gabatar da ƙarin shaidu domin tabbatar da zarge-zargen da ake yi masa.
