Kofin Duniya: Moroko za ta kara da Kanada bayan cire Holland a zagayen ‘yan 32

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙasar Moroko ta doke ɗaya daga cikin ƙasashen ake hasashen ka iya lashe gasar Kofin Duniya da fari, wato Netherlands bayan an tashi 3 da 2 a zangon bugun da kai sai mai tsaron gida a wasan da aka gudanar a tsakaninsu.

Hakan ya biyo bayan tashi a wasan 1 da 1, bayan shafe mintina 120 ana gumurzu a filin wasa, lamarin da ya ba wa ƙasar Afirkan nasarar tsallakewa zuwa zagayen ‘yan 16.

Ɗan wasa Cody Gakpo ne ya fara zura ƙwallo a ragar Moroko a lokacin da aka kai minti na 72, yayin da Issa Diop ya farke a minti na 91 bayan samun ƙwallo daga Chemsdine Talbi.

Ismael Saibari ne ya zura ƙwallon da ta ba Moroko nasara a bugun fenaratin.

A yanzu dai Atlas Lions za ta kara da Kanada a ranar 4 ga watan Yuli a zagayen ‘yan 16.

By Babaji

Leave a Reply