Sojoji sun ceto ɗalibai 10 sa’o’i bayan Boko Haram ta farmaki makaranta a Borno

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Dakarun tsaron Nijeriya sun yi nasarar ceto ɗalibai guda 10 da aka yi garkuwa da su a makarantar sakandare ta Lassa da ke Ƙaramar Hukumar Askira-Uba a Jihar Borno sa’o’i bayan da ‘yan ta’adda suka farmaki makarantar yayin da ake tsaka da rubuta jarrabawar NECO a ranar Litinin.

Rahotanni sun bayyana cewa, maharan sun je makarantar ne a akan babura, inda suka yi garkuwa da ɗaliban kana daga bisani dakarun Atisayen Haɗin Kai suka ƙaddamar da atisayen bincike da ceto ta taimakon jiragen sama na yaƙi.

A wata sanarwa da jami’in yaɗa labaran sojoji na riƙo na Dakarun Haɗin Kai, Kyaftin Mohammed Goni ya fitar, rundunar ta ce ta tura sojoji cikin hanzari zuwa yankin yayin da ta samu rahotannin harin.

A cewarsa, an yi amfani da jirgin sama na yaƙi da bayanan sirri wajen tura jami’ai da agajin wasu daga ƙasa, lamarin da ya bayar da damar farauto ‘yan ta’addar da suka tsere da kuma ceto ɗaliban.

Ya ce, a yayin atisayen ceton an yi ba-takashi tsakanin dakarun tsaron da ‘yan ta’addar a yankin Daggu.

Kakakin sojin ya ƙara da cewa soja guda da wani mamban jami’an haɗaka na CJTF sun rasa rayukansu a yayin karanbattan.

Sanarwar ta bayyana cewa, atisayen ya yi sanadiyyar ceto ɗalibai guda 10 da aka same su cikin aminci, waɗanda a halin yanzu suke karɓar kulawar da ta dace.

Kazalika, Goni ya ce ana cigaba da ƙoƙarin ganin an ceto sauran waɗanda aka sacen da kuma tabbatar da dukkan masu hannu a harin sun fuskanci hukuncin doka.

By Babaji

Leave a Reply