Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Gwamnan jihar Kebbi, Malam Nasir Idris ya ƙaddamar da aikin kamfanin Lot 7–ZANE, mai samar da wutar lantarki mai aiki da hasken rana a Kebbi.
Da ya ke jawabi yayin ƙaddamar da aikin a garin Ambursa jiya Lahadi, Gwamna Nasir Idris, ya ce gwamnatin sa ta himmatu wajen haɗa hannu da hukumar samar da wutar lantarki ta yankunan karkara domin inganta samar da ayyuka masu inganci a ɓangaren wutar lantarki kuma ana sa ran samar da wutar lantarki mai karfin 33kV a wannan yankin.
Ya ƙara da cewa, aikin samar da wutar lantarki mai karfin megawatt 3.5 na jihar, wanda hukumar samar da wutar lantarki ta karkara ke aiwatarwa, zai inganta samar da wutar lantarki a faɗin jihar Kebbi.
Gwamnan ya bayyana wutar lantarki a matsayin ginshiƙin cigaban tattalin arziki na zamani da samar da tsaftataccen makamashin hasken rana mai karfin megawatts 3.5, wanda ke tallafawa na’urorin adana batir da zai tabbatar da samun wutar lantarki ko da bayan faɗuwar rana.
Gwamna Idris ya yabawa hukumar raya wutar lantarki ta karkara da takwarorinta, Kelm Elicon Joint Venture, waɗanda ta hanyar su ne ake gudanar da aikin.
Ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar Kebbi ta samar da wurin aikin kyauta ga kamfanin Kelm Elicon Joint Venture, sannan ya buƙaci ‘yan kwangilar da su yi aiki mai inganci cikin wa’adin da aka ƙayyade.
Gwamnan ya kuma yi kira ga al’ummar garin Ambursa da su rungumi aikin, da kiyaye kayayyakin aiki, tare da bayar da cikakken haɗin kai ga ‘yan kwangila da ma’aikata zuwa lokacin kammala aikin.
Da ya ke jawabi tun da farko, babban manajan hukumar raya wutar lantarki ta karkara, Injiniya Abba Abubakar Aliyu, ya bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince wa hukumar da dalar Amurka miliyan 750 don aiwatar da ayyukan ƙananan cibiyoyi masu alaƙa da juna a faɗin ƙasar nan.
Ya yi bayanin cewa kimanin dalar Amurka miliyan 10 ne za a zuba a wannan aikin na jihar Kebbi, wanda ake sa ran zai amfana fiye da gidaje 1,000 da suka haɗa da filin jirgin saman Ahmadu Bello da ke Birnin Kebbi ta hanyar inganta wutar lantarki.
Ali Kobeissi, babban jami’in hukumar Kobeissi Electrical and Mechanical Engineering Ltd. ya bada tabbacin cewa za’a kammala aikin nan da watanni takwas masu zuwa kamar yadda aka shata tare da kira ga al’ummomin da suka amfana da su taimaka wajen ganin an gudanar da aikin cikin nasara.
