Daga ALI ABUBAKAR SADIQ
Amurka ta fara yakin Iran da tsammanin za ta murkushe su cikin makonni biyu, ko matuka a makonni uku. Ta hanyar muggan hare haren bama bamai a kasar tare da kashe shugabannin Iran, wanda su ke tsammanin zai haifar da tarzomar Iraniyawa ga gwamnatin su wanda zai tilasta su mika wuya.
Me ya sa tsarin na Amurka ya kasa wanzuwa cikin nasarar da su ka tsammata? Ku san kowannenmu idan zai tuna yarinyarsa a makaranta ko a unguwa, akasari mun san wani mai cin zali (bully) da ya yi sharafinsa. Shi mai cin zali za ka samu kato ne ko mai karfi da yake da Yara masu goya masa baya, da masu tsoronsa ko a malamai. Ana masa biyayya ko ba don Allah ba. To, amma wata Rana idan aka sami wani sabon yaro, mara tsoro mai juriya, idan fada ya hada su, daga wannan ranar alkadarin mai cin zali ke rushewa.
Ba domin wannan sabon yaro zai lallasa mai cin zali ba ne, domin ba shi da wannan karfin. Amma domin ya yarda ya fuskanci mai cin zalin, ya shanye duka da kutufon sa, ya ki mika masa wuya har Dan din zalin ya gaji ya nemi a tsaida fadan. Shi sabon yaro asararsa daya ce, wato jikinsa zai yi tsami, amma mai cin zali zai rasa sunan da ya gina na tsawon lokaci, za a daina tsoronsa duk wata kima ta sa za ta rushe, abubuwa na alfarma da ya daɗe ya na ci a ɓagas za su kauce, a bar shi shi kadai.
To, Iran wannan ‘strategy’ ta yi amfani da shi wajen cin nasarar wannan yaki fiye Amurka. Na farko yakin ya dinke mutanen kasar waje guda sakamakon sadaukar da ran da Ali Khamenei ya yi. Amurka sun yi asarar kuɗaɗe da makaman yaƙi da ba su taɓa yi ba. Iran ta rushe sansanonin Amurka da ke gabas ta tsakiya, sun ratattaka Israila. Amurka da kanta ta nemi tsagaita wuta a dawo teburi saboda sun kusa karar da makaman yakinsu wadanda ba za su iya maye gurbinsu a Dan kankanin lokaci ba.
Babbar nasarar Iran wadda ba a taba zaton za ta yi tasiri ba, duk da cewa Iran ta gargadi Amurka a kan ta idan an kai mata hari, wato shine na rufe mashigin Hormuz. Wannan ne ya zama makami mafi girma da Iran ta samu sakamakon wannan yaƙi.
To, ina aka dosa? Shin za a tsayar da yakin ko za a ci gaba? Amurka ta yi asara mafi muni a shekaru 60, amma ba za ta iya karbar cewa ta fadi a wannan yaki ba. Burin Amurka shine na mallakar ikon tsibirin Kharg da man Iran. Wannan kwadayi da alama a nan gaba kadan zai sa, maimakon Amurka ta kirga asararta ta koma gida, za ta sake ƙoƙarin tsunduma kanta, ta sake nutsewa cikin wannan ciniki mara riba da ta ɗauko a Iran na ƙoƙarin tura sojojin ƙasa.
Abin sani shine cewa, tun shekaru 25 da su ka gabata, ƙasar Iran ke shirye-shiryen karbar bakuntar sojojin kasa a cikin kasarta, ganin yadda Amurka ta mamaye Iraq. To amma Amurka ta sani cewa, Iran ba Iraq ba ce, kuma yakin kwana 40 ya nunawa Duniya cewa Iran a shirye ta ke. Sai kun zo!!!
