SUBEB ta fara horas da malamai 2,500 a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Hukumar ilimin bai ɗaya da makarantun sakandare ta Jihar Katsina ta fara gudanar da shirin horas da malamai da shugabannin makarantu 2,500 a babbar makarantar KCK da ke Katsina, domin ƙara inganta ingancin koyarwa da jagorancin makarantu a faɗin jihar

Ana gudanar da horaswar tare da haɗin gwiwar British Council da Education Solutions Ltd, ƙarƙashin shirin Strengthening Teachers’ English Proficiency (STEP) da kuma Instructional Leadership Programme, a ƙarƙashin jagorancin kwamishinan ma’aikatar ilimin firamare da sakandare ta Jihar Katsina, Hon. Yusuf Sulaiman Jibia.

Da yake jawabi a wajen buɗe taron, Hon. Yusuf Sulaiman Jibiya ya bayyana cewa shirin zai horas da malamai 2,000 da shugabannin makarantu 500 domin haɓaka ƙwarewarsu a harshen Turanci, tare da ƙarfafa dabarun jagorancin makarantu. Ya ce hakan zai taimaka wajen bunƙasa ingancin koyarwa da ilmantarwa a makarantun gwamnati da masu zaman kansu a jihar.

A cewarsa, za a gudanar da horon a cibiyoyin bunƙasa Malamai (Teachers Development Centres) da ke Katsina da Daura.

Ma’aikatar ta yi maraba da dukkan mahalarta taron, tana mai bayyana cewa wannan shiri wani muhimmin mataki ne na gwamnatin jihar wajen inganta ilimi da haɓaka ƙwarewar malamai da shugabannin makarantu.

Malamai daga makarantu masu zaman kansu ma suna cikin waɗanda ke cin gajiyar wannan horo. Sun bayyana jin daɗinsu tare da yabawa gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, PhD, bisa wannan kyakkyawan tsari da ya haɗa su cikin shirin domin su ma su amfana, wanda zai taimaka wajen ƙara inganta koyo da koyarwa ga ɗalibai a faɗin jihar.

A halin yanzu, ana ci gaba da gudanar da taron horaswar a babbar nakarantar KCK da ke cikin birnin Katsina, inda mahalarta ke samun horo kan dabarun koyarwa na zamani da inganta jagorancin makarantu.

By ukarofi

Leave a Reply