Akalla mutane 94 sun mutu bayan wani jirgin ruwa mallakin gwamnatin Zimbabwe ya kife a tafkin Kariba, yayin da gwamnati ta tabbatar da cewa jirgin na ɗauke da fasinjoji fiye da karfin da aka tanada masa.
Jirgin ruwan ya kife ne a makon da ya gabata yayin da yake kan hanyarsa daga garin Kariba zuwa wata al’umma da ke zaune a wani yanki mai nisa na tafkin. Rahotanni sun ce guguwar ruwa mai karfi ce ta bugi jirgin, lamarin da ya sa ya kife.
Gwamnatin Zimbabwe ta ce jirgin na ɗauke da kusan mutane 180 tare da kaya a lokacin da hatsarin ya faru. Adadin ya ninka karfin fasinjojin da ‘yan sanda suka bayyana a baya, inda suka ce jirgin bai kamata ya ɗauki fiye da mutane 90 ba.
Zuwa ranar Talata, ‘yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutane 94, yayin da aka ceto wasu 77. Hukumomi sun ce har yanzu ana ci gaba da aikin bincike da kwaso gawawwakin waɗanda suka rasa rayukansu.
Hatsarin ya zama mafi muni a tarihin haɗurran sufuri na Zimbabwe, a cewar jaridar gwamnatin ƙasar The Herald. Ya zarce hatsarin motar bas da ya faru a shekarar 1991, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 89.
Tafkin Kariba, wanda ke kan iyakar Zimbabwe da Zambia, na daga cikin manyan tafkunan da mutum ya kirkira a duniya. Masu aikin ceto da kwaso wadanda hatsarin ya rutsa da su sun ci gaba da aikin a bakin tafkin yayin da hukumomi ke ƙoƙarin gano sauran waɗanda suka bace.
