
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Dakarun Rundunar Sojin Nijeriya sun yi nasarar halaka ‘yan ta’addan Boko Haram guda 21 yayin wani samame a sansaninsu da ke yankin Tsaunin Kopre na Ƙaramar Hukumar Hong a Jihar Adamawa.
Wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa an gudanar da atisayen ne a tsakanin 26 da 27 ga Agusta, bayan samun wani rahoton leƙen asiri da ya nuna cewa akwai mayaƙan ƙungiyar a yankin. A cewarta, sojojin sun je yankin ne a yanayi na sanɗa kafin suka ƙaddamar da hare-hare a yankin tsaunin na Kopre.
Zagazola Makama ya ce atisayen ya yi sanadiyyar mutuwar ‘yan Boko Haram 21, yayin da wasu suka tsere da raunukan harbin bindiga. Sojojin sun lalata maɓoyar ‘yan ta’addan ciki har da kayan gudanar da harkokinsu na yau da kullum da suka samu a yankin.
Haka kuma, sun ƙwato makamai da dama yayin atisayen, ciki har da bindigogin AK-47 da mazubin alburusansu da kuma alburusan 7.62mm. Majiyar ta ƙara da cewa, sojojin sun kuma lalata babura, kekunan hawa da jarkokin masu ƙunshe da fetur na ‘yan ta’addan.
Ɗaya daga cikin mambobin mafarauta da suka yi wa sojojin rakiya ya rasa ransa yayin arangamar, kamar yadda rahotanni suka shaida.

