
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Cibiyar Tsaron Amurka, Pentagon, ta shirya janye kimanin dakarunta guda 200 daga Nijeriya waɗanda aka tura ƙasar a wannan shekarar domin yaƙi da ƙungiyoyin “tsatstsauran ra’ayin addinin Islama”, kamar yadda New York Times (NYT) ta ruwaito.
Jami’an Amurka da Nijeriya sun shaida wa jaridar cewa tawagar dakarun da aka tura ta samar da sakamakon da aka yi tsammani.
A cewar rahoton da NYT ta fitar a ranar Alhamis, wasu daga cikin tawagar dakarun za su cigaba da kasancewa domin cigaba da taimaka wa ayyukan leƙen asiri da horar da ƙananan jami’ai.
Jami’an Amurka sun bayyana shirin tura dakarun zuwa Nijeriya a matsayin wani tsari ga goben atisayensu a Nahiyar Afirka.
