Ma’aikatan lafiya a Katsina za su fara yajin aikin gargaɗi a faɗin jihar

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Hadaddiyar ƙungiyar ma’aikatan lafiya ta Jihar Katsina (AHAPN) ta sanar da shirin fara yajin aikin gargaɗi na kwanaki bakwai daga ranar Talata, 8 ga watan Satumba, 2026.

A cewar ƙungiyar, yajin aikin zai shafi mambobin ƙungiyoyin ma’aikatan lafiya daban-daban, ciki har da masana kimiyyar magunguna, ma’aikatan jinya da ungozoma, da kuma masana kimiyyar ɗakunan gwaje-gwaje.

Ƙungiyar ta ce ta yanke shawarar shiga yajin aikin ne sakamakon sakamakon gazawar gwamnati na biyan wasu buƙatun da suka gabatar ciki har da aiwatar da tsarin albashi da wasu alawus-alawus na ma’aikatan lafiya.

AHAPN ta ce idan ba a warware matsalolin da suka gabatar ba bayan kammala yajin aikin gargadin, za ta iya ɗaukar matakin shiga yajin aikin sai baba-ta-gani.

Ƙungiyar ta buƙaci al’ummar jihar da su fahimci mataki da dalilin da yasa suka ɗauki matakin shiga yajin aiki.

By ukarofi

Leave a Reply