Blueprint ta taya Ikenna Okonkwo murnar sake zaɓen sa a matsayin Babban Sakataren SWAN

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar gudanarwar Kamfanin Jaridun Blueprint, ta taya Sakatare-Janar na Ƙungiyar Maruwaita Labaran Wasanni ta Ƙasa (SWAN), Ambasada Ikenna Okonkwo bisa sake zaɓar sa a muƙamin wanda ke cikin kwamitin zartarwar ƙungiyar.

Hukumar ta isar da saƙon taya murnar ne a lokacin da aka gabatar wa Okonkwo takarar shaidar sake samun muƙamin a gare shi a babban ofishinta da ke Abuja a ranar Litinin.

Shugaban kamfanin, Mallam Salisu Umar tare da Daraktan Editanci, Mista Clem Oluwole da kuma Mallam Gambo Abdullahi, wato babban jami’in kula da lamuran kuɗaɗe ne suka haɗu wajen taya shi murnar.

Haka kuma, hukumar ta bayyana sake zaɓar Okonkwo a matsayin tasirin jagorancinsa, ƙoƙari da gudummawa ga ci-gaban aikin jarida da ya shafi wasanni da ci-gaban SWAN da ya ke bayarwa.

Okonkwo dai shi ne editan kafafen sada zumunta na jaridar Blueprint.ng, wanda ke ƙoƙarin sauke nauye-nauyen da suka rataya a wuyansa bisa ƙwarewa.

An sake zaɓar sa ne a karo na biyu a muƙamin yayin babban taron da SWAN ta gudanar a Kaduna na 2026, inda mambobinta suka zaɓi sabon kwamitin zartarwa na ƙasa da zai jagoranci harkokinta na tsawon shekaru uku.

By Babaji

Leave a Reply