‘Yan sanda sun kama ƙarin mutum biyu ɗauke da buhunan abincin Tamuwa a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Rundunar ‘yan sanda a Katsina sun kama ƙarin mutum biyu a bincike da suke gudanarwa kan yadda ake karkatar da abincin RUTF da aka fi sani da ‘yar ƙwamaso.

‘Yar ƙwamaso abincin ƙananan yara ‘yan ƙasa da shekara biyar masu fama da rashin abincin gina jiki wanda gwamnnatin tarayya da hukumar UNICEF da sauraren ƙungiyoyin sa kai suka samar.

A baya dai ‘yan sanda sun kama Muhamud Aliyu ɗauke da buhu uku na ‘yar ƙwamaso wanda bincike na farko wanda ake zargi ya ambaci sunan Zaharaddin Musa wani jami’in kiwon lafiya da ‘yan sanda suke nema ruwa a jallo.

A cigaba da bincike, ‘yan sanda sun ƙara kama wasu mutum biyu Buhari Idris ɗan shekara 40 da Idris Abdullahi ɗan shekara 51 da laifi na ƙoƙarin karkatar da abincin yara masu fama da cutar ƙwamaso.

Wannan abincin gina jiki kyauta ake ba yara amma ana zargin wasu ɓata gari da haɗin kan wasu jami’an kiwon lafiya sukan karkatar da abincin zuwa kasuwa.

Kwamishinan ‘yan sanda a Katsina CP Ali Umar Fage ya gargaɗi mutane musamman jami’an kiwon lafiya da su guje karkatar da kayan gwamnnatin tarayya musamman irin wannan abincin gina jiki na ƙananan yara masu fama da cutar Tamuwa.

By ukarofi

Leave a Reply