
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Shirya Jarrabawar Neman shiga Manyan Makarantu JAMB, fitar da sakamakon jarrabawar UTME ga ɗaliban da shekarunsu bai kai yadda aka iyakance wa masu son shiga manyan makarantu ba.
Saidai hukumar ta ce kasancewar ta fitar da sakamakon, hakan ba ya nufin ɗaliban sun cancanci samun gurbi a makarantun ba ne, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
A wata sanarwa da Daraktan hulɗa da jama’ar hukumar, Fabian Benjamin a ranar Asabar, hukumar ta ce ta fitar da sakamakon ne domin bai wa ɗalibai da iyayensu damar sanin makin da suka samu a UTME.
Ta kuma ce, ba za a yi amfani da su ba wajen samun gurbi a manyan makarantu har sai ɗalibi ya cika sharaɗin da ake buƙata na abin da ya shafi adadin maki, shekaru da sauransu.
Kazalika, JAMB ta ce ɗaliban da suka samu makin da ake buƙata kuma suka cika sharaɗin kaiwa shekara 16 zuwa sama ne kaɗai za a ba wa gurbi a manyan makarantu.
