Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ma’aikatar Harkokin Ruwa da Tattalin Arzikin Teku ta Nijeriya ta samar da kuɗaɗen shiga har Naira tiriliyan 1.83 a shekarar 2025, lamarin da ke nuna ƙarin kashi 160 cikin 100 idan aka kwatanta da Naira biliyan 700.79 da aka samu a shekarar 2023.
Ministan Harkokin Ruwa da Tattalin Arzikin Teku, Adegboyega Oyetola, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja. Ministan ya ce ɓangaren harkokin ruwa na Nijeriya ya samu gagarumin sauyi cikin shekaru uku da suka gabata, tun bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kafa Ma’aikatar Harkokin Ruwa da Tattalin Arzikin Teku a watan Agustan 2023.
A cewar Oyetola, ma’aikatar ta ɗauki matakan gaggawa wajen amfani da damar tattalin arzikin da ke cikin gabar tekun Nijeriya mai tsawon kilomita 853, da kuma faɗaɗɗun hanyoyin ruwa na cikin ƙasa, domin mayar da tattalin arzikin ruwa da albarkatun teku zuwa ginshiƙin samar da kuɗaɗen shiga, bunƙasa kasuwanci, inganta tsaro da samar da ayyukan yi.
Yayin gabatar da rahoton nasarorin da ma’aikatar ta samu cikin shekaru uku, Oyetola ya ce shirin garambawul ɗin da aka aiwatar ya haifar da ci gaba mai auna gaske a fannoni da suka haɗa da samar da kuɗaɗen shiga, inganta ababen more rayuwa a tashoshin jiragen ruwa, tsaron teku, tsara dokoki, bunƙasa harkokin jigilar kaya da jiragen ruwa na ’yan Nijeriya, haɓaka ƙwarewar ma’aikata, kamun kifi da kuma tsaron hanyoyin ruwa na cikin ƙasa.
Ya ce, babban manufar ma’aikatar ita ce mayar da dimbin albarkatun ruwa da Nijeriya ke da su zuwa tattalin arziki mai ɗorewa da zai amfani ’yan Nijeriya. Oyetola ya bayyana gagarumin ƙarin kuɗaɗen shiga da hukumomin da ke ƙarƙashin ma’aikatar suka samu a matsayin ɗaya daga cikin manyan alamomin ci gaban da aka samu.
Ya danganta wannan ƙaruwa da sauye-sauyen dokoki da tsarin gudanarwa, ƙarfafa hanyoyin tabbatar da tattara kuɗaɗen shiga, amfani da fasahar zamani wajen gudanar da ayyuka, da kuma rufe hanyoyin da ake zargin kuɗaɗen gwamnati na ɓacewa ta cikinsu.
Ya ce ingantaccen tsarin samun kuɗaɗen shiga na daga cikin wani babban shiri na gina tattalin arzikin harkokin ruwa wanda yake da gaskiya, inganci kuma mai jan hankalin masu zuba jari.
