‘Yan daba sun farmaki ‘yan jarida bayan gangamin APC a Kano

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Asabar wasu da ake zargin ‘yan daba ne suka ƙaddamar da farmaki akan ‘yan jarida guda biyar da ‘yan sanda uku a Jihar Kano jim-kaɗan bayan ɗaukar rahoton gangamin jam’iyyar APC.

Al’amarin ya auku ne a yankin Ƙofar Nassarawa ta bayan farfajiyar Jami’ar Maitama Sule, wadda aka fi sani da North West University yayin da ‘yan jaridar suke kan hanyar koma wa ofisoshinsu daga filin wasa na Sani Abacha, inda aka gudanar da taron.

An yi zargin cewa maharan sun kai wa mutanen farmakin ne da adduna da wuƙaƙe, inda suka yi ta sarar motar gidan Rediyo Nijeriya da ke ɗauke da ‘yan jarida da ‘yan sandan, wanda hakan ya sa suka farfasa gilashin motar da wasu sassanta.

Wani ɗan jarida da ke aiki da Pyramid FM mai suna Yakubu Abubakar Gwagwarwa, wanda ya tabbatar da faruwar al’amarin, ya ce kasancewar akwai ‘yan sanda uku a motar hakan bai tsorata ‘yan dabar ba.

Ya ce, akwai ma’aikatan Pyramid FM guda huɗu a motar, sai wani ɗan jarida daga Guarantee Radio da kuma ‘yan sandan, waɗanda aka rage wa hanya daga filin taron.

Gwagwarwa ya ƙara da cewa, a lokacin da maharan suke saran motar direban ya juya da baya domin tserewa, inda suka bi su tare da raunata direban a lokacin da suka fasa gilashin tagogin motar.

Har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoto, rundunar ‘yan sandan jihar ba ta fitar da saƙo kan lamarin ba.

By Babaji

Leave a Reply