Dalilin da ya sa kamfanin Uber ya fice daga Nijeriya bayan shekaru 12 – FAAN

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD

Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Tarayya ta Nijeriya (FAAN) ta musanta cewa tana da hannu wajen ficewar kamfanin jigilar fasinjoji ta manhajar Uber daga Nijeriya, tana mai cewa matakin da kamfanin ya ɗauka na iya kasancewa sakamakon la’akari da yanayin tattalin arziki da dokokin da suka shafi harkokinsa.

Idan za a iya tunawa cewa Uber ta dakatar da ayyukan jigilar fasinjoji ta manhajarta a Nijeriya daga ranar 2 ga Satumba, 2026, bayan shafe shekaru 12 tana gudanar da ayyukanta a ƙasar.

Manajan Daraktar FAAN, Olubunmi Kuku, ta ce duk da haka hukumar ta samu koke-koke a lokacin hutun Kirsimeti na watan Disamba dangane da munanan abubuwan da wasu fasinjoji suka fuskanta wajen amfani da wasu kamfanonin jigilar fasinjoji ta manhaja da kuma motocin haya a filayen jiragen sama.

Kuku ta bayyana hakan ne yayin bikin shigar da sabbin mambobi karo na biyu da kuma buɗe hotunan waɗanda aka karrama a zauren mashahuran ’yan harkar sufurin jiragen sama na Nijeriya, wato Nigeria Aviation Hall of Fame, da aka gudanar a Legas.

Taken taron shi ne: “Sabbin Shugabannin Gaba a Harkar Sufurin Jiragen Sama: ƙwarewa, Fasaha da Gasa a Duniya.” Ta ce, wasu fasinjoji sun kai rahoton fuskantar barazana da tsoratarwa daga wasu direbobi, yayin da wasu aka sauke su a wuraren da ba su nufa ba, baya ga wasu koke-koke.

Ta ƙara da cewa, FAAN ta samu saɓani da wasu kamfanonin jigilar fasinjoji ta manhaja kan alhakin da ya rataya a wuyan direbobi da kuma samar da wuraren musamman da direbobin ke ɗaukar fasinjoji a filayen jiragen sama.

Kuku ta ce: “A cikin ’yan makonnin nan, na ga bayanai da dama a kafafen yaɗa labarai, kuma ina ganin yana da muhimmanci mu fayyace wasu abubuwa. Ina aiki ne a FAAN, kuma babban alhakin da ke kaina shi ne tabbatar da cewa fasinjojinmu suna cikin aminci, ana kare su, sannan suna samun sauƙin gudanar da tafiyarsu.”

Dangane da ficewar Uber, ta ce ba za ta iya magana a madadin kamfanin ba, tana mai cewa tana da yaƙinin cewa Uber ta yi la’akari da abubuwan da suka shafi tattalin arziki da dokoki ne kafin ta yanke shawarar ficewa daga Nijeriya.

Sai dai ta ce abin da ya fi muhimmanci ga FAAN shi ne tabbatar da cewa an magance matsalolin da fasinjoji ke fuskanta.

“A lokacin hutun Disamba, mun samu koke-koke da dama daga fasinjojin da suka yi amfani da wasu motocin jigilar fasinjoji ta manhaja da kuma motocin haya, inda suka fuskanci munanan abubuwa. Wasu sun ce an tsoratar da su, wasu kuma an sauke su a wuraren da ba su nufa ba, har ma da wasu abubuwan da suka fi haka muni,” inji ta.

Manajan Daraktar ta kuma bayyana cewa akwai lokutan da wasu direbobin Uber da Bolt ke barin motocinsu da sunan za su shiga filin jirgin sama a matsayin direbobin jigilar fasinjoji ta manhaja, amma sai su shiga harkar motocin haya domin karɓar kuɗin da ya fi yadda aka saba.

Ta ce, saboda yawan koke-koken da ake samu kan ayyukan masu neman fasinjoji a filin jirgin sama, FAAN ta ga ya dace ta ƙara sanya ido da tsari kan harkar motocin haya. Ta ce, manhajar Airport Car Hire Rank Management System (ACHRAMS) da hukumar ta ƙirƙira an samar da ita ne domin tabbatar da cewa fasinjoji suna iya gano kamfanonin motocin haya da direbobin da ke aiki a filayen jiragen sama.

Kuku ta jaddada cewa FAAN ba ta karɓar kuci a madadin direbobin motocin haya, sannan direbobin ba ma’aikatan hukumar ba ne. Ta ce, aikin FAAN shi ne kawai bai wa fasinjoji damar sanin kamfanin ko direban da zai ɗauke su, tare da samar musu da misalin farashin da ake caji bisa ga inda suke son zuwa.

Ta kuma bayyana cewa motocin haya na filayen jiragen sama a dabi’ance suna karɓar kuɗi mafi tsada, saboda direban kan kai fasinja daga filin jirgin sama zuwa wani wuri sannan ya dawo filin jirgin ba tare da samun wani fasinja a dawowar ba.

A cewarta, fasinja ne ke da zaɓin ko zai yi ajiyar mota tun kafin lokaci, ko ya yi amfani da manhajar jigilar fasinjoji, ko kuma ya yi amfani da motar haya ta filin jirgin sama.

Ta ce FAAN ba ta da ikon tilasta wa fasinja amfani da ɗaya daga cikin hanyoyin, sai dai alhakin hukumar shi ne tabbatar da cewa fasinja ya san wanda zai tuka shi da kuma mutanen da ke gudanar da ayyuka a cikin filin jirgin.

Dangane da saɓanin da FAAN ta samu da kamfanonin jigilar fasinjoji ta manhaja, Kuku ta ce babban abin da ya jawo matsalar shi ne batun alhaki idan wani abu ya faru.

Ta ce kamfanonin sun nemi a ware musu wuraren ɗaukar fasinjoji na musamman a filayen jiragen sama, abin da FAAN ta amince da shi, amma hukumar ta buƙaci kamfanonin su cauki alhakin direbobin da ke aiki da su.

Sai dai a cewarta, an sha gaya wa hukumar cewa direbobin ba ma’aikatan Uber ba ne, domin direbobi ne masu zaman kansu.

“Saboda haka, duk wata damuwar tsaro da muka nuna, sun ce fasinjoji su yi amfani da hanyoyin tsaro da ke cikin manhajar. Ba sa son su ɗauki wannan alhakin, kuma wannan ya zama babbar matsala a tsakaninmu,” inji Kuku.

By ukarofi

Leave a Reply