APC za ta samu nasara a 2027 – Sanata Yari

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD Gusau

Sanata Abdulaziz Yari, wanda kuma shine darakta janar na majalisar yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027, ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa Jam’iyyar All Progressives Congress, APC, za ta lashe zaɓe mai zuwa.

Ya bayyana hakan yayin da yake magana da manema labarai a yau Juma’a a gidansa da ke Talata Mafara a Zamfara.

Yari ya ce yaƙin neman zaɓen jam’iyyar na 2027 za su ta’allaƙa ne kan nuna nasarorin cigaban tattalin arzikin gwamnati shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

A cewar tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Shugaba Tinubu yana ci gaba da jajircewa wajen farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya duk da ƙalubalen da ake fuskanta a yanzu.

“Majalisar yaƙin neman zaɓen 2027 za ta nuna manyan nasarorin da aka samu wajen inganta tsarin tattalin arzikin ƙasar,” in ji Yari.

“Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya himmatu wajen haɓaka tattalin arziki da kuma kafa harsashin ci gaba mai ɗorewa.” Ya ƙara da cewa.

Ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su goyi bayan takarar Tinubu na neman wa’adi na biyu, yana mai jayayya cewa ci gaba yana da mahimmanci don ƙarfafa gyare-gyaren da ake ci gaba da yi da kuma kai ƙasar zuwa manyan matakai na ci gaba.

Yari ya kuma yi kira ga ‘yan APC a Zamfara da kuma a faɗin jihohi 36 da su ci gaba da haɗin kai tare da goyon bayan majalisar kamfen ta hanyar wayar da kan jama’a.

“Za mu yi aiki ba tare da gajiyawa ba don tabbatar da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dawo kan mulki a 2027 kuma ya kayar da dukkan abokan hamayya cikin gamsuwa,” in ji shi.

Sanatan ya jaddada cewa haɗin kai a cikin jam’iyyar da kuma wayar da kan masu jefa ƙuri’a zai zama mabuɗin tabbatar da nasarar Jam’iyyar APC a zaɓen da ke tafe.

Ana sa ran gudanar da babban zaɓen 2027 a watan Fabrairun 2027.

By ukarofi

Leave a Reply