
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jam’iyyar African Action Congress (AAC) ta yi alla-wadai da mummunan kisan da aka yi wa Ibrahim Khalil Ɗan Shagamu, wato ɗan Soshiyal Mediya kuma mai sharhi kan al’amuran siyasa da gwamnati, wanda rasuwarsa ta zo ƙarshe a gidansa da ke Gaida a Ƙaramar Hukumar Kumbotso da ke Jihar Kano.
Abokin tafiyar ɗan takara shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC, Haruna Garba Magashi ne ya bayyana haka ga manema labarai a ranar Alhamis a Kano.
A cewarsa, wannan al’amari abin firgitarwa ne kuma mai raɗaɗi ga makusanta da al’umma, wanda gabanin haka ya koka kan barazana ga rayuwarsa ga gwamnatin Jihar Kano da hukumomin tsaro musamman ‘yan sanda na su ba shi kariya. “Ya buƙaci kariya. Ya gargaɗi hukumomin cewa rayuwarsa tana cikin haɗari. Duk da haka, kariyar ba ta je gare shi ba. Yau ga shi ya rasu,” inji Magashi.
Ya bayyana cewa, akwai buƙatar gwamnati ta yi bayanin abin da ya faru kan yadda aka yi ba a ɗauki matakan da suka dace ba bayan ya yi magiya kan a ba shi kariya.
Haruna Magashi ya ce matsayinta na jam’iyya mai ƙoƙarin bayar da kariya ga ‘yancin ɗan-adam, adalci da biyayya ga hukunce-hukuncen doka, AAC ta ayyana kisan Ɗan Shagamu a matsayin abin da ba za a lamunta ba da ya haddasa ƙunci a zukata.
Akan haka ne ta yi tir da gwamnatin Kano da hukumomin tsaro bisa gazawarsu na bayar da kariya ga marigayin a lokacin da ya buƙaci a kai masa ɗauki. Kazalika, ta ce wajibi ne a zurfafa bincike akan al’amarin tare da gurfanar da dukkan waɗanda aka samu da hannu a ciki a gaban doka, tana mai kira da a tabbatar da gaskiya da adalci yayin haka.
