
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta cika alƙawarin da ta yi na karrama tawagar manyan ‘yan wasan kwando na mata, D’Tigress biyo bayan nasarar lashe gasar ƙwallon kwando na mata na Afirka na 2025 da Hukumar Ƙwallon Kwando ta Ƙasa-da-ƙasa FIBA ta shirya.
A wata sanarwa da Hukumar Kula da Wasanni ta Ƙasa NSC, ta fitar a ranar Laraba, ta ce an bai wa kowace ‘yar wasa Dala 100,000, wato kwatankwacin Naira miliyan 132.6, yayin da aka bai wa jami’an tawagar Dala 50,000 kowannensu.
Hukumar ta tabbatar da cewa, an yi biyan ne a ranar 9 ga Satumba, 2026 kuma dukkan ‘yan wasa da jami’an sun sanar da cewa sun karɓi kuɗaɗen nasu. Wannan ya nuna cewa an cika alƙawarin da Shugaba Bola Tinubu ya yi wa tawagar bayan lashe kofunan Afrobasket karo na bakwai a tarihinta kuma sau biyar a jere.
A wata takarda da Kakakin NSC, Kehinde Ajayi ya fitar, hukumar ta bayyana cewa ladar karramawar ta kuma ƙunshi kyautar ƙasa ta OON da gida mai ɗakin barci guda uku ga kowanne a Abuja.
An ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ne da kansa ya sanya wa takardun gidajen da kyautar OON ɗin hannu kuma an damƙa su ga tawagar a watan Fabarairun 2026 yayin wasannin neman gurbi a kofin duniya na FIBA World Cup a Lyon, ƙasar Faransa.
