
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya nufi zuwa birnin New Delhi da ke ƙasar Indiya domin wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a taron jagororin ƙasashen BRICS karo na 18, inda zai nemi a ƙarfafa alaƙar tattali da difulomasiyya da muhimman ƙasashe.
Taron, wanda aka tsara gudanarwa a ƙarshen makon nan a Bharat Mandapam na New Delhi, zai haɗa jagororin BRICS da ƙasashe masu hulɗa da ita da kuma ɗaiɗaikun mutane masu alfarma da aka gayyata daga sassa daban-daban na duniya domin tattauna ci-gaban tattali a matakin duniya da alaƙoƙin lamuran ci-gaba.
Nijeriya ta shirya amfani da damar babban taron ne wajen ƙarfafa dabarunta na harkokin tattali da cimma wasu manufofin diflomasiyya. Kakakin mataimakin shugaban ƙasa, Stanley Nkwocha ne ya sanar da zuwan Shettima taron a wata takarda da ya fitar a ranar Juma’a.
A cewar Fadar Shugaban Ƙasa, Nijeriya za ta yi amfani da taron wajen faɗaɗa alaƙoƙin ci-gaba da ke tsakaninta da wasu ƙasashe, faɗaɗa haɗin-gwiwar harkar tattali da bunƙasa dabarunta musamman akan kasuwanci da zuba jari, makamashi, noma, albarkatun ƙasa da kuma ƙirƙira.
Haka kuma, BRICS na 18 zai samar wa Nijeriya wani fage na ciyar da haɗin-gwiwar da ke tsakaninta da ƙasashe masu tasowa.
Taken taron na 2026 shi ne “Building for Resilience, Innovation, Cooperation and Sustainability”, inda Nijeriya za ta cimma matsaya a fannonin haɗin kai a lamuran siyasa, tsaro, tattali da kuɗi da kuma musayar al’adu da jama’a ga jama’a.
Shigar Nijeriya wannan taro ya yi daidai da ƙoƙarin Shugaba Tinubu na ƙarfafa alaƙoƙin Nijeriya da ƙasashen waje da kuma janyo ra’ayin masu zuba jari da buɗe karin wasu kasuwanni ga kayayyakin ƙasar.
