Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da hukuncin shekaru 490 kan tsohon shugaban bankin NEXIM

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta tabbatar da hukuncin da aka yanke wa tsohon Manajan Daraktan Bankin Fitar da Kayayyaki na Nijeriya (NEXIM Bank), Robert Orya, kan zargin almundahanar Naira biliyan 2.4.

News Point Nigeria ta ruwaito cewa kotun ta yi watsi da ƙarar da Orya ya ɗaukaka, tare da tabbatar da hukuncin da Kotun ƙoli ta Babban Birnin Tarayya (FCT) da ke Abuja ta yanke masa kan tuhume-tuhume 49.

Kotun ta yanke wa Orya hukuncin zaman gidan yari na shekaru 10 kan kowanne daga cikin tuhume-tuhumen 49, wanda idan aka tara zai zama shekaru 490. Sai dai kotun ta bayar da umarnin gudanar da hukuncin a lokaci guda, ma’ana hukuncin da zai yi aiki a zahiri shi ne shekaru 10.

Hukuncin ya fito ne daga kwamitin alkalai uku da Mai Shari’a Muhammed Danjuma ya jagoranta, tare da Mai Shari’a Ntong Festus Ntong da Mai Shari’a Ele Ejo Enenche, inda suka yanke hukunci baki ɗaya.

Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arziƙin ƙasa Zagon ƙasa (EFCC), ta hannun kakakinta, Dele Oyewale, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Talata.

Orya ya kasance Manajan Daraktan NEXIM Bank daga shekarar 2009 zuwa 2016. Marigayi Shugaba Umaru Yar’Adua ne ya naɗa shi a matsayin shugaban bankin a ranar 14 ga Agustan 2009, sannan tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ya sake naɗa shi a ranar 18 ga Agustan 2014.

Bayan barinsa mukamin, EFCC ta gurfanar da Orya a shekarar 2021 kan tuhume-tuhume 49 da suka shafi karɓar kuɗi ta hanyar yaudara, ƙirƙirar takardu da kuma damfarar kuɗin da aka ce sun kai Naira biliyan 2.4.

Daga bisani, Kotun ƙoli ta FCT da ke Abuja ta same shi da laifi kan dukkan tuhume-tuhumen 49, inda ta yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekaru 490 a ranar 5 ga Fabrairun 2026. An umurci a gudanar da hukuncin a lokaci guda, wanda hakan ya sa hukuncin da zai yi aiki a zahiri ya zama shekaru 10.

Bai gamsu da hukuncin Mai Shari’a F.E. Messiri na Kotun ƙoli ta FCT ba, sai Orya ya garzaya Kotun ɗaukaka ƙara domin neman a soke hukuncin da aka yanke masa.

A hukuncin da ta yanke ranar Talata, kwamitin alkalai uku ya ce alƙalin kotun farko ya yi daidai wajen same shi da laifi, yana mai cewa masu gabatar da ƙara sun tabbatar da shari’ar tasu ba tare da wata shakka mai ma’ana ba.

Mai Shari’a Danjuma, wanda ya jagoranci sauran alkalan biyu wajen yanke hukuncin baki ɗaya, ya ce:

“Na yi nazarin dukkan bayanan da lauyoyi suka gabatar, sannan na duba bayanan shari’ar kotun farko, tare da batutuwan da wannan kotu ta tsara domin warware wannan ƙara.

“Na duba kowane batu ɗaya bayan ɗaya, kuma a ƙarshe, dukkan batutuwan da aka gabatar domin yanke hukunci a kansu sun koma ga wanda ake ƙara a kan mai ɗaukaka ƙara. Wannan ƙara ba ta da wani ingantaccen dalili, saboda haka an yi watsi da ita.

“Hukuncin Kotun ƙoli ta Babban Birnin Tarayya da aka yanke a ranar 5 ga Fabrairu, 2026, a cikin shari’ar mai lamba FSC/SC/CS/487/2021, an tabbatar da shi.”

Hukuncin Kotun ɗaukaka ƙara ya tabbatar da ci gaba da kasancewar hukuncin da Kotun ƙoli ta FCT ta yanke wa tsohon shugaban NEXIM Bank, ciki har da hukuncin zaman gidan yari na shekaru 10 da zai yi aiki a zahiri.

By ukarofi