Sojoji sun kama jagoran ‘yan ta’adda da wata mai safarar alburusai a Kaduna

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuj

Dakarun tsaro na Atisayen FANSAR YAMMA a Arewa maso Yamma, sun yi nasarar kama mutane da dama da ake zargi da hannu a ta’addanci da kuma ƙwato wani ƙunshin alburusai yayin atisaye daban-daban a Jihar Kaduna.

Rundunar sojoji ta ce, an gudanar da atisayen ne a ranar Laraba, 9 ga Satumba a ƙananan hukumomin Kubau, Igabi da Birnin Gwari a jihar.

A safiyar Laraba, dakarun sashi na 1 sun gudanar da atisaye a yankin Dabar Dabo, wanda sojoji suka bayyana a matsayin maɓoya ga ‘yan ta’adda a Ƙaramar Hukumar Kubau. A yayi haka an kama jagoran ‘yan ta’adda da wasu mutum biyu da ake zargin ‘yan dabarsa ne. Tuni aka garzaya da su komar rundunar domin gudanar da bincike akansu.

A wani atisayen kuma a ranar, sojoji sun yi nasarar kama wata mata mai kimamin shekaru 50 ɗauke tarin alburusai a Karamar Hukumar Igabi bayan samun wani bayanin sirri. A cewar soji, an samu matar da alburusai guda 300 da aka ƙunshe a cikin wata jaka.

Bincike ya nuna cewa, matar ta yi tafiya daga Zamfara zuwa Lafia a Jihar Nasarawa, inda aka yi zargin ta karɓo alburusan domin kai wa ‘yan ta’adda a Birnin Gwari, Jihar Kaduna. A yanzu haka tana hannun sojoji ana cigaba da gudanar da bincike akanta.

Daga bisani a ranar, dakarun sashi na 1 tare da haɗin-gwiwar ‘yan bijilante, sun kama wani da ake zargin yana aikin samar wa ‘yan ta’adda kayan amfanin yau da kullum a Birnin Gwari. Yayin binciken sa, sojoji sun ƙwato wasu na’urorin sadarwa guda huɗu da ake zargin ‘yan ta’adda suna amfani da su wajen gudanar da harkokinsu. Shi ma da abin da aka ƙwato a hannunsa suna komar sojoji don cigaba da bincike.

Rundunar ta ce waɗannan atisaye na nuna ƙoƙarin dakarun FANSAN YAMMA na katse hanyoyin ayyukan ta’addanci, taƙaice zirga-zirgar masu taimaka wa ‘yan ta’adda da safarar makamai da wasu kayayyaki.

Jami’an haɗakar sun kuma yaba wa al’umma bisa haɗin kan da suke ba su, inda suka yi kira a gare su da su kasance masu lura da ruwaito dukkan wani abin zargi ga hukuma mafi kusa.

By Babaji

Leave a Reply