INEC za ta binciki zargin almundahanar malaman jami’a da za su gudanar da zaɓen 2027

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta ce za ta binciki zarge-zargen nuna son kai ga ’yan siyasa da ake yi wa wasu malaman jami’o’i da ka iya zama jami’an gudanar da zaɓe a babban zaɓen 2027, sannan ta ɗauki matakin da ya dace bisa sakamakon binciken.

Daraktar Ilimantar da Masu Zaɓe da Yaɗa Labarai ta hukumar, ɓictoria Ita-Messi, ce ta bayyana hakan a wata tattaunawa da ’yan jarida a ranar Laraba, yayin da take martani kan damuwar da aka nuna game da yiwuwar ɗaukar malaman jami’o’in da suka fito fili suka bayyana goyon bayansu ga wasu ’yan takarar siyasa.

An bayyana goyon bayan ne a wani taron tattaunawa da Mai Ba Shugaban ƙasa Shawara Kan Harkokin Siyasa, Ibrahim Masari, ya shirya a Kaduna.

Taron, wanda aka gudanar a Cibiyar Umaru Musa Yar’Adua da ke Kaduna, ya haɗa manyan malamai da masana, jami’an gwamnati da ’yan siyasa domin duba ayyukan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da tattauna alƙiblar siyasar ƙasar gabanin zaɓen 2027.

Sai dai Ita-Messi ta ce caukar malaman jami’o’i aiki a matsayin jami’an zaɓe wani tsari ne da hukumar ta tanada, tana mai cewa duk wani rahoto da ya shafi zargin nuna son kai kan ɗaya daga cikin malaman za a bincika shi. “ɗaukar malaman jami’o’i aiki wani tsari ne na hukumar,” inji ta.

Ta ƙara da cewa, hukumar za ta duba rahotannin, ta tabbatar da sahihancin zarge-zargen, sannan ta ɗauki matakin da ya dace bisa abin da binciken ya tabbatar, wanda za a bayyana wa jama’a.

Jawabin na INEC ya biyo bayan damuwar da wasu ’yan adawa da ƙungiyoyin siyasa suka nuna, ciki har da Atiku Abubakar, Peter Obi da African Democratic Congress (ADC), kan dacewar amfani da malaman jami’o’in da ake zargin suna da alaƙar siyasa a matsayin jami’an gudanar da zaɓe a 2027.

Atiku ya yi gargaɗin cewa bai kamata a yi amfani da malaman jami’o’in da ke nuna son kai ga ’yan siyasa a matsayin jami’an zaɓe ba.

Shi kuwa Peter Obi, ta hannun ofishin yaɗa labaransa, ya ce abin damuwa ne yadda wasu malaman jami’o’i, waɗanda INEC ke amfani da su a matsayin Jami’an Tattara Sakamakon Zaɓe da Jami’an Bayyana Sakamako, ke bayyana goyon bayansu ga ’yan siyasa a fili.

A wata sanarwa da mai magana da yawun Peter Obi Media Reach (POMR), Idris Zekeri, ya fitar ranar Talata, ya ce abin da ke faruwa na iya zama yunƙurin tun da wuri na gina da kuma halalta wata hanyar amfani da masu nuna son kai ga jam’iyyu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

A nata ɓangaren, ADC ta nuna damuwa kan yiwuwar ɗaukar malaman jami’o’in da suka fito fili suka goyi bayan ’yan takarar siyasa domin gudanar da muhimman ayyukan zaɓe.

A wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na ƙasa na jam’iyyar, Malam Bolaji Abdullahi, ya sanya wa hannu ranar Litinin, ADC ta ce malamai, kamar sauran ’yan Nijeriya, suna da ’yancin da kundin tsarin mulki ya ba su na goyon bayan ɗan takarar da suke so.

Sai dai jam’iyyar ta ce bai kamata a ɗora wa waɗanda suka bayyana matsayinsu na siyasa a fili alhakin gudanar da ayyukan zaɓe masu muhimmanci da ka iya shafar sakamakon zaɓen da ’yan takarar da suke goyon baya ke fafatawa ba.

ADC ta buƙaci INEC ta kafa tare da wallafa ƙa’idoji bayyanannu na zaɓen Jami’an Bayyana Sakamako da Jami’an Tattara Sakamakon Zaɓe, ciki har da matakan da za su hana mutanen da suka taɓa bayyana goyon bayan wani ɗan takara ko shiga harkokin siyasar jam’iyya gudanar da muhimman ayyukan zaɓe.

Jam’iyyar ta kuma buƙaci hukumar ta wallafa sunayen mutanen da ake shirin naɗawa a matsayin jami’an tattara da bayyana sakamako tun da wuri, domin jam’iyyu da sauran jama’a su samu damar bayyana duk wata damuwa ta gaskiya da za ta iya tasowa dangane da yiwuwar samun saɓanin muradi.

ADC ta ce sahihancin zaɓe bai dogara kawai da halayen masu zaɓe da ’yan takara ba, har ma da tsakani da rashin son kai na waɗanda aka ɗora wa alhakin gudanar da zaɓe, tattara sakamako da bayyana shi.

By ukarofi

Leave a Reply