2027: Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da sahihancin rajistar NDC a matsayin jam’iyyar siyasa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kotun Ɗaukaka Ƙara a Abuja, ta jingine hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ya umarci a soke rajistar jam’iyyar NDC a matsayinta na jam’iyyar siyasa a Nijeriya.

A yayin hukuncin, wanda alƙalai uku suka jagoranta, kotun ta tabbatar da matakin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) na amincewa da NDC, tana mai ayyana hukuncin babbar kotun na ranar 26 ga Yuli a matsayin rashin biyayya ga hukuncin doka.

Sannan, ta ce hukuncin na baya cin fuska ne ga ikon doka da matakan shari’a wanda ya kuma saɓa wa hukuncin da kotun ɗaukaka ƙarar ta yi ranar goma ga Disambar 2025 da ya amince tare da tabbatar da sahihancin rajistar NDC da INEC ta yi.

Haka kuma, kotun ta ta yi watsi da iƙirarin cewa bajen jam’iyyar ba ainihin nata ba ne na jam’iyyar Peace Movement Party ce, yana mai tabbatar wa NDC tare da amincewa buƙatarta ta bayar da tabbacin sahihancin rajistarta.

Saidai ɗaya daga cikin alƙalan mai suna Mai Shari’a Okon Abang ya nuna cikakken goyon baya da amince wa hukuncin babbar kotun na soke rajistar NDC a matsayin jam’iyyar siyasa, yana mai cewa kotun ta yi amfani da matakan doka wajen yanke hukuncin nata.

By Babaji

Leave a Reply