An zargi wata mata da halaka mijinta kan shirin ƙara aure a Kano

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

An kama wata mata, Bilkisu Sani a Ƙaramar Hukumar Rogo da ke Jihar Kano kan zargin ta da halaka mijinta mai suna Hafizu Gausu, wanda aka ce yana shirin ƙara aure.

Auwal Kazagi, wanda mazaunin yankin ne, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa al’amarin ya auku ne a ranar Juma’a da misalin ƙarfe 7 na yamma a unguwar Katsalle na cikin garin Rogo. Ya ce, mazauna sun hanzarta zuwa gurin domin gane da idanunsu bayan jiyo kuka daga matar Gausu, wadda ta yi iƙirarin cewa an yanka mijinta.

“A lokacin da muka isa wajen, mun ga cewa ba yanka shi aka yi ba, buga masa wani abu aka yi a kai. Ya shiga halin zubar da jini sannan ya rasu. Kuma akwai alamar cizo a kunnensa,” inji Kazagi. Ya ƙara da cewa, an kira ‘yan sanda sun je sun tafi da gawar domin gudanar da bincike akanta.

Sannan, mazaunin ya ce ana zargin mamacin yana soyayya da wata mace da shirin auren ta a matsayin matarsa ta biyu, lamarin da ya haifar da rikici tsakaninsa da Bilkisu, wadda ta ci alwashin hana faruwar auren. Da fari dai manyan sun shiga tsakani, amma kuma al’amarin ya yi ƙamari daga bisani.

Kazagi ya kuma ce, ‘yan sanda sun kama Bilkisu a matsayin ainihin wadda ake zargi da hannu a mutuwar mijin nata yayin da ake cigaba da bincike. A safiyar ranar Asabar ne aka yi wa marigayin jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Bayanai sun nuna cewa, ma’auratan sun kasance mata da miji na tsawon shekaru bakwai, inda Allah ya albarkace su da ‘ya’ya biyu kuma a yanzu haka tana ɗauke da wani juna biyu na marigayin mijin nata. Majiyoyi sun ce, saboda nuna rashin amincewarta ne ya sa Gausu ya nemi gidan wadda ya son aura su ɗage auren da wata biyu kan yadda aka tsara da farko.

By Babaji

Leave a Reply