Direba ya kuɓuta bayan biyan miliyan N2 yayin da ‘yan bindiga suka buƙaci fansar N30m ga limaman Zamfara shida

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

‘Yan bindigar da suka yi awon-gaba da malamai guda shida a Jihar Zamfara sun buƙaci a biya su Naira miliyan 30 a matsayin kuɗin fansa domin sako su.

Rahotanni sun bayyana cewa, wani mai suna Malam Muhammad Ibrahim a ƙauyen Dakka na Ƙaramar Hukumar Bakura, ya tabbatar wa jaridar Daily Trust wannan ci-gaba ta wayar tarho. Saidai ya ce direban da aka sace tare da limaman ya shaƙi iskar ‘yanci bayan biyan ‘yan bindigar Naira miliyan 2.

Ya ce, “Yan bindigar sun sace jimillar mutum takwas ne – limamai biyar, direbansu da wasu mutane biyu da ke kan hanyar koma wa gida daga gona.” Ya kuma ce, Naira 300,000 da jarkokin fetur biyu masu cin lita 25 ne ‘yan bindigar suka buƙaci a ba su domin sako sauran mutane biyun.

Ya bayyana cewa, yayin da direban ya koma cikin iyalansa a ƙauyen Kwatsama, ana shirin biyan miliyan N30 domin sako limaman da aka yi garkuwa da su tare. A cewar wata majiya mai ƙarfi, wani sanata mai ci a jihar Zamfara ya yi alƙawarin biyan kuɗin fansar domin sako limaman, tana mai cewa “muna fatan hakan ba zai ɗauki lokaci ba.”

Malam Ibrahim, ya kuma roƙi hukumomi da su ƙara ƙaimi wajen ƙoƙarin ceto malaman, inda ya ce akwai yiwuwar ana cin zarafinsu ta hanyar lakaɗa musu duka, kuma saboda shekarunsu hakan ka iya zama barazana ga lafiyarsu.

Sunayen limaman dai sune kamar haka: Malam Muhammadu Shehu, Babban Limamin Masallacin Juma’a na Dakko; Malam Murtala Dakko, mataimakinsa; Malam Muhammad Yahuza, Babban Limamin Masallacin Juma’a na Dogon Madacci na farko; Malam Magawata Abdullahi, Babban Limamin Masallacin Juma’a na Dogon Madacci na biyu; Malam Bala Hogun, Babban Limamin Masallacin Juma’a na Hogun; da kuma Babban Limamin Masallacin Juma’a na Kwatsama, wato Malam Muhammad Tasi’u.

An dai yi awon-gaba da waɗannan limamai ne a ranar Asabar na makon da ya gabata a ƙauyen Gidan Bature da ke Gundumar Damri a Ƙaramar Hukumar Bakura, a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka yi musu kwanton-ɓauna. Wata majiya ta ce al’amarin ya faru ne a lokacin da malaman suke kan hanyar zuwa Talatan Mafara domin halartar wani zama a gidan Sanata Abdulaziz Yari.

By Babaji

Leave a Reply