Cibiyar kula da cututtuka masu yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) ta ce ta ƙara tsaurara matakan sa ido da shirin ko-ta-kwana bayan gwamnatin Kenya ta tabbatar da ɓullar cutar Ebola da aka shigo da ita daga Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC). Cutar dai ta samo asali ne daga kwayar Bundibugyo virus, kuma NCDC na ci gaba da sa ido kan halin da ake ciki a yankin.
A cewar sanarwar NCDC ta ranar 6 ga Oktoba 2026, wanda ya kamu da cutar ɗan ƙasar Kenya ne da ya taɓa zama a Kongo. Ya yi tafiya ta hanya daga Kongo zuwa Kampala a Uganda, daga nan ya tashi zuwa Nairobi inda aka keɓe shi tare da gudanar da gwaji da ya tabbatar da kamuwa da cutar. Daga bisani mara lafiyan ya rasu, yayin da hukumomin Kenya suka fara binciken waɗanda suka yi mu’amala da shi. NCDC ta jaddada cewa har zuwa ranar 6 ga Oktoba 2026, babu wani tabbataccen mai cutar Ebola a Najeriya.
NCDC ta ce tana aiki tare da ma’aikatar lafiya ta tarayya, hukumomin lafiya a tashoshin jiragen ruwa, gwamnatocin jihohi da sauran abokan hulɗa wajen ƙarfafa shirin kare Najeriya daga cutar. Matakan sun haɗa da gano cutar da wuri, keɓe waɗanda ake zargi, gwajin ɗakunan bincike, binciken waɗanda suka yi mu’amala da marasa lafiya, yaɗa sahihan bayanai da kuma kare ma’aikatan lafiya. Hukumar ta kuma buƙaci jama’a su kasance cikin natsuwa amma su ƙara taka-tsantsan, tare da kula da tsaftar hannu da guje wa hulɗa da jinin ko ruwan jikin wanda ake zargin yana da cutar.
Hukumar ta kuma shawarci ma’aikatan lafiya da su kasance cikin shiri musamman idan sun ga mara lafiya mai alamomin da su kai kama da Ebola kuma yana da tarihin tafiya ko hulɗa da wanda ya kamu da cutar cikin kwanaki 21 da suka gabata. Matafiya daga wuraren da ake fama da cutar kuma an buƙace su da su sanya ido kan lafiyarsu na tsawon kwanaki 21, sannan su nemi kulawar lafiya cikin gaggawa idan alamomi sun bayyana. NCDC ta ce za ta ci gaba da sa ido kan abubuwan da ke faruwa a Kenya, Kongo da sauran ƙasashen da abin ya shafa, tare da ƙarfafa shirye-shiryen Najeriya gwargwadon buƙata.
