Ya kamata a samar da tsarin bai-ɗaya na cigaban Arewa – Gwamna Uba Sani ga manya yankin

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi kira ga jiga-jigan siyasar Arewa da su fi mayar da hankali wajen samar da wani tsari na bai-ɗaya da zai magance matsalolin da yankin ke fuskanta, maimakon mayar da hankali kan neman karɓe iko a matakin tarayya.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da shugabannin Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello suka kai masa ziyarar ban-girma a ranar Laraba, a zauren Majalisar Zartarwa na Gidan Gwamnatin Jihar Kaduna. Ya nuna godiyarsa ga gidauniyar bisa yadda take jan hankalin ’yan siyasar Arewa da masu riƙe da muƙaman gwamnati kan muhimmancin mayar da hankali ga muhimman batutuwan da suka shafi bunƙasa jarin ɗan Adam, yana mai cewa yankin Arewa ba shi da wata manufa ta bai-ɗaya da ke jagorantar cigabansa.

Gwamna Uba Sani ya ce, taron Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello da ke tafe, wanda taken sa shi ne “Ingantaccen Mulki, Masana’antu da ƙirƙire-ƙirƙire, da kuma Ci Gaba Mai ɗorewa”, ya zo a daidai lokacin da ake matuƙar buƙatar irin wannan tattaunawa. Ya ce, “Ina farin ciki da ganin Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello tana jagorantar wannan yunƙuri, domin muna buƙatar mu zauna tare, mu duba matsalolinmu sannan mu nemo hanyoyin magance su gaba ɗaya.”

Gwamnan ya kuma nuna damuwarsa kan yawan mace-macen mata masu juna biyu da jarirai a Arewacin Nijeriya, tare da ƙara jaddada matsalar yawan yaran da ba sa zuwa makaranta da kuma ƙarancin ilimin sana’o’i da ƙwarewa a yankin. Ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta fi mayar da hankali kan kiwon lafiya na matakin farko, musamman wajen tabbatar da cewa talakawa da mazauna yankunan karkara sun samu damar samun kulawar lafiya, ba tare da yin watsi da kiwon lafiya na mataki na biyu ba. “Mu a Kaduna, mun yi imanin cewa samun ingantaccen kiwon lafiya haƙƙi ne na kowa, musamman marasa galihu da masu rauni a cikin al’umma,” inji shi.

Gwamnan, wanda ya ambaci alƙaluman Asusun Tallafa wa Yara na Majalisar ɗinkin Duniya (UNICEF), ya ce akwai kusan yara miliyan 18 da ba sa zuwa makaranta a Nijeriya, inda kashi 70 cikin 100 daga cikinsu ke zaune a Arewacin ƙasar.

Ya ce lokacin da ya karɓi mulkin Jihar Kaduna, akwai sama da yara 500,000 da ke yawo a tituna ba tare da zuwa makaranta ba, amma zuwa yanzu gwamnatinsa ta mayar da kusan 360,000 daga cikinsu zuwa makarantu daban-daban. Uba Sani ya bayyana cewa tsarin da Jihar Kaduna ta ɓullo da shi na tantance gidaje domin gano yaran da ba sa zuwa makaranta, ya samu karɓuwa daga Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, wadda ta ɗauke shi a matsayin abin koyi wajen tunkarar matsalar a faɗin ƙasar.

Dangane da ilimin sana’o’i da ƙwarewa, Gwamnan ya ce Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya aike masa da wasiƙa kimanin watanni uku da suka gabata, inda ya nemi Jihar Kaduna ta bai wa Gwamnatin Tarayya damar amfani da tsarin da jihar ta samar.

Ya bayyana cewa, Jihar Kaduna ta kafa Cibiyar Horar da Sana’o’i da Bunƙasa ƙwarewa, wadda ke da rassa a Soba, Rigachikun da Samarun Kataf, domin hidimtawa yankunan sanatoci na Arewa, Tsakiya da Kudancin jihar.

A cewarsa, cibiyar tana koyar da sana’o’in da suka shafi fasahar sadarwa da kwamfuta (ICT), mekatroniks da makamashi mai sabuntawa, ta yadda za a haɗa ilimi kai tsaye da samun aikin yi, kasuwanci da sabbin masana’antun da ke tasowa.

Ya ce cibiyar ta riga ta horar da sama da masu sana’a 4,000, abin da ya bayyana a matsayin wani gagarumin mataki wajen rage rashin aikin yi da bunƙasa ƙwarewar matasa. “Yanzu muna shirin karɓar kusan mutane 32,000, wanda hakan ke nufin cewa a cikin shekara guda muna da damar horar da sama da matasa 30,000, sannan a ba su takardar shaidar kammala horo da za ta ba su damar yin aiki a ko ina a duniya,” inji Gwamnan.

Yayin da yake jawabi tun da farko, tsohon Gwamnan Jihar Neja, Dakta Mu’azu Babangida Aliyu, wanda ya jagoranci tawagar gidauniyar, ya gode wa Gwamna Uba Sani bisa ware wa gidauniyar fili mai girman hekta 50 domin kafa Jami’ar Haɗin Kan Arewa (Arewa Unity University).

Aliyu ya kuma tuna cewa marigayi Gwamnan Jihar Kaduna, Patrick Yakowa, ya taɓa bai wa gidauniyar wani fili da ke kusa da dandalin Murtala Mohammed Sƙuare, inda daga baya aka gina ofishinta. Ya bayyana cewa za a gudanar da taron Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello a ranar 28 ga Oktoba, 2026, inda Gwamna Uba Sani zai kasance babban mai masaukin baƙi kuma baƙon girma na musamman a wajen taron.

By ukarofi

Leave a Reply