Mayar da hannun agogo baya ne dawo da tallafin fetur – APC ga ‘yan adawa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jam’iyyar APC ta yi watsi da batun dawo da tallafin fetur, inda ta ƙalubalanci ‘yan takarar shugaban ƙasa na tsagin adawa da su yi bayanin yadda za su samar da kuɗaɗen tsarin ba tare da tauye kuɗaɗen shigar da gwamnati take samu ba da kuma sauke wajiban suke kanta na kuɗi.

Sakataren Jam’iyyar na Ƙasa, Sueajudeen Ajibola Basiru ne ya faɗi haka a ranar Juma’a, inda ya bayyana cire tallafin fetur a matsayin abin da ba zai yiwu ba, sannan ya yi gargaɗin cewa muddin aka dawo da shi, Nijeriya za ta koma gidan jiya ta yadda za ta riƙa fafutukar yadda za ta warware matsalolin kuɗi cikin sauƙi.

Basiru ya furta waɗannan kalamai ne a lokacin da ya karɓi wasu ‘yan takara da suka fice daga jam’iyyun ADC da NDC su 10 suka dawo APC mai mulki. “Ministan Man Fetur ya ce ba za mu koma wa tallafi ba. Ya tafi kenan har abada,” inji Basiru.

Ya ce, matakin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na cire tallafin fetur ya rage wa gwamnati matsin kuɗi da inganta ƙarfin kuɗin gwamnatocin tarayya da na jihohi wajen sauke nauye-nauyen da suka rataya akansu.

Haka kuma, ya tunatar da yadda wasu gwamnatocin jihohi suke fafutukar biyan albashin ma’aikata da ‘yan fansho wanda hakan ya kai su ga ciyo bashi domin warware waɗannan matsaloli da wasunsu gabanin cire tallafi.

Kazalika, sakataren ya ƙalubalanci ‘yan adawa da su bambance tsakanin tallafin fetur da tsare-tsaren farashi, yana mai cewa bai dace a riƙa mu’amalantar ababe biyun a matsayin abu guda ba.

By Babaji

Leave a Reply