Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Jami’an ‘yan sanda sun sami nasarar kama wani direba da ba a bayyana sunan sa ba wanda ya buge wani mai babur a hanyar Birnin Kebbi zuwa Argungu da ke jihar Kebbi.
Ganau Malam Abdullahi Muhammed Dagwaya ya bayyanawa wakilin mu da cewa sun tsaya Sallah a ƙauyen Gidan Hamani ne wannan babbar motar ta zo ta wuce, bayan sun gama Sallah suka fara tafiya, sun kusa shigowa garin Argungu sai suka tarar da wannan motar a gaban su ta ture wannan mai babur ɗin kuma ta ja shi ƙasa wanda ya yi sanadiyyar mutuwar sa nan take.
Sai dai ya bayyana rashin jin daɗin sa bisa yadda direban ya nuna halin ko oho saboda haka nan take ya kira wayar ɗaya daga cikin ‘yan sanda da ke Argungu ya shaida masa abinda ke faruwa, ba su yi ƙasa a gwiwa ba ba suka nufi hanyar Sokoto suka taro direban zuwa chaji ofis da ke garin Argungu.
Ya ƙara da cewa an sami tabbacin mai babur din mutumin garin Lailaba ne da ke sana’ar achaɓa a garin Birnin Kebbi kuma yana kan hanyar sa ne ta komawa gida.
Wakilin mu ya nemi jin ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar Kebbi Sufurtanda Bashir Usman sai dai bai ɗauki waya ba kuma har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton bai mayar da saƙon kar-ta-kwana ba.
