
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rahotanni daga Kudu maso Yammacin Nijeriya sun bayyana cewa, wasu ‘yan bindiga sun afka wa cibiyar bincike ta Cocoa Research Institute of Nigeria (CRIN) da ke Jihar Oyo, sannan suka sace manyan jami’ai guda uku yayin da suke tsaka sa binciken tsirrai a wata gona da ke farfajiyar cibiyar.
Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar al’amarin a ranar Juma’a, 9 ga Oktoba, 2026, inda ta tabbatar wa al’umma cewa an fara ƙoƙarin ceto mutanen cikin aminci da kama masu hannu a laifin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, Olayinka Ayanlade ne ya tabbatar da labarin a wata takarda da ya fitar Ibadan, babban birnin jihar inda ya ce an yi garkuwa da mutanen ne a lokacin da suke bakin aiki a cibiyar. Akan haka ne rundunar ta gaggauta tura jami’ai domin fara aikin ceto waɗanda al’amarin ya rutsa da su yayin da ta samu rahoton.
Haka kuma, hukumar ta jaddada wa al’umma cewa ana ɗaukar dukkan matakan da suka dace wajen warware matsalar tare da kira ga jama’a akan su ruwaito wa ofishin ‘yan sanda mafi kusa wani bayani da aka san zai taimaka wa atisayen ceton ko ta hanyoyinta na isar mata da saƙon gaggawa.
Wannan na zuwa ne yayin da shiyyar ke fuskantar barazanar hare-haren garkuwa da mutane, inda a kwanan nan aka yi awon-gaba da wasu daga cikin ‘yan hidimar ƙasa (NYSC) a Jihar Imo, waɗanda suka taso daga Ibadan a Jihar Oyo da nufin zuwa jihohin Abia da Akwa-Ibom domin karɓar horo. Rahotanni sun nuna cewa su 30 ne a lokacin da al’amarin ya faru, inda guda 10 daga cikinsu suka yi nasarar tserewa kafin a garzaya da su daji. Amma daga bisani jami’an tsaro sun yi nasarar ceto sauran 20 ɗin ba tare da an biya kuɗin fansa ba, kamar yadda rundunar ‘yan sandan Imo ta bayyana.
