Mawaƙiya Ayra Starr ta zama ’yar Afirka ta farko da ta jagoranci nishaɗin hutun wasan NFL

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Mawaƙiyar Najeriya, Oyinkansola Sarah Aderibigbe, wadda aka fi sani da Ayra Starr, ta kafa sabon tarihi bayan ta zama ’yar Afirka ta farko da ta jagoranci shirin nishaɗin hutun wasan gasar ƙwallon ƙafa ta Amurka, NFL International Games.

Ayra Starr ta gabatar da wasan ne a ranar Lahadi, 11 ga Oktoba, lokacin da ƙungiyoyin Philadelphia Eagles da Jacksonville Jaguars suka fafata a filin wasa na Tottenham Hotspur da ke Landan, Birtaniya.

Mawaƙiyar ta buɗe shirin da waƙarta mai suna Heaven Baby, kafin ta ci gaba da rera Santa, Rush da Dangerous. Ta kammala wasan da haɗa waƙoƙin Hot Body da Ms. Paper.

Wannan nasara ta nuna yadda waƙoƙin Afrobeats ke ƙara samun karɓuwa a manyan dandamalan nishaɗi na duniya, musamman a wajen Afirka, inda mawakan nahiyar ke samun damar gabatar da fasaharsu a gaban masu sauraro daga ƙasashe daban-daban.

Ayra Starr ta kuma bayyana wannan nasara a shafinta na X, inda ta jaddada cewa ita ce ’yar Afirka ta farko da ta jagoranci irin wannan shirin a gasar NFL International Games.

Tun bayan da ta fara samun karɓuwa a shekarar 2020, Ayra Starr ta gina suna a masana’antar kiɗa ta duniya. Kundin waƙoƙinta na farko, 19 & Dangerous, wanda ta fitar a shekarar 2021, ya taimaka wajen ƙara fito da ita a idon duniya.

Waƙoƙinta irin su Rush, Bloody Samaritan da Commas sun kuma taimaka wajen faɗaɗa masu sauraron waƙoƙinta a ƙasashe da dama.

By ukarofi

Leave a Reply