
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu ta bayyana muradinta na son cigaba da zama a Fadar Shugaban Ƙasa a Abuja har zuwa shekarar 2031.
Ta bayyana haka ne yayin ƙaddamar hedikwatar tafiyar PBAT Door-to-Door Movement a Abuja, wato tafiyar da aka kafa domin wayar da kan jama’a a yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Ahmed a zaɓen 2027 a matakin tushe. “Ina son barin Aso Rock a 2031 da yardar Ubangiji, kuma na shiga Nijeriya a lokacin ina farin ciki a matsayin mai shekaru 70 da ɗoriya,” inji ta.
Ta bayar da misali da ci-gaban da aka samu a filayen jiragen saman Nijeriya a matsayin ɗaya daga cikin nasarorin da gwamnatinsu ta samar, inda ta ce tana son ta riƙa tafiye-tafiye a halin walwala.
A yayin taron, Sanata Oluremi ta ƙaddamar da hedikwatar tafiyar sannan ta sadaukar wa yiwuwar nasarar shugaban ƙasar a zaɓen 2027. Kazalika, ta bayyana godiyarta nisa goyon baya ga jam’iyyar APC da kuma Gwamnatin Ekpemupolo, wanda aka fi sani da Tompolo, wato jagoran tafiyar.
Ana ganin waɗannan kalamai na uwargidan shugaban a matsayin bayar da kariya a bainar jama’a ga salon jagorancin mijinta tun kafin ya zama shugaban ƙasa kuma ya cigaba akan haka yayin da ake cigaba da tafka muhawara kan tasirin tsare-tsaren mulkinsa akan al’umma da ma ƙasa baki ɗaya.
A shekarar 2022 ne dai a lokacin da Oluremi Tinubu, wadda Sanatan Legas ta Tsakiya ce, ta bayyana ƙwarin-gwiwa kan ƙwarewar mijin nata a Legas zai taimaka masa wajen warware matsalolin Nijeriya, waɗanda da dama daga cikinsu sun jima suna haddasa ƙalubale kan al’amuran yau da kullum acikin al’ummar ƙasa.
