Cikar farin dangon jama’a a Kaduna ya nuna yadda Arewa maso Yamma ta amince da tazarcen Tinubu, inji Iliyasu Kwankwaso

Spread the love

Jigo a kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Musa Illiyasu Kwankwaso, ya bayyana cewa yankin Arewa maso Yamma na goyon bayan sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2027, yana mai kafa hujja da yawan mutanen da suka halarci gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a Kaduna da kuma goyon bayan da suka nuna masa.

Da yake magana da manema labarai a yayin gangamin a gefen rumfar manyan baƙi (VIP Pavilion), Kwankwaso ya ce yadda aka tattara magoya baya Kuma al’umma suka yi cikar farar dango ya kawar da shakku kan matsayar siyasar Arewa maso Yamma gabanin zaɓen 2027.

A cewar Kwankwaso, “Taron ya nuna aniyar yankin na marawa Tinubu baya domin ya yi wa’adi na biyu, kuma wannan goyon baya na a matsayin wani alƙawari na ƙarfafa haɗin kan ƙasa da gina Najeriya mafi inganci”.

“Yau, mu al’ummar yankin Arewa maso Yamma, mun bayyana matsayarmu karara kan wanda muke goyon baya. Zaɓinmu na Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana nuna jajircewarmu wajen ganin an samu Najeriya mafi inganci da haɗin kan ƙasa,” in ji Kwankwaso.

Ya yi ikirarin cewa sake zaɓen Tinubu zai bada damar ƙarfafa ci gaba mai adalci tare da tabbatar da raba albarkatun ƙasa cikin daidaito tsakanin yankunan siyasa guda shida na Najeriya.

Ya kara da cewa gwamnatin Tinubu na ƙoƙarin daidaita muradun yankuna daban-daban na ƙasar, yana mai fatan samun ci gaban ƙasa ta hanyar ƙarfafa goyon bayan Arewa maso Yamma.

“Shugabancin Tinubu yana wakiltar raba albarkatu cikin adalci da daidaito ga dukkan yankuna, kuma komawarsa kan mulki zai zama alheri ga babbar Najeriya da muke fata,” in ji shi.

Kwankwaso ya kuma ƙi amincewa da ra’ayin cewa goyon bayan Arewa ga Tinubu ya samo asali ne kawai daga wata yarjejeniya ta siyasa da za ta amfani wani ɓangare. Ya jaddada cewa yankin a shirye yake ya cika alƙawarin siyasar da ya ɗauka yayin da babban zaɓe na gaba ke ƙaratowa.

“Asiwaju shi ne ɗan takarar Arewa, kuma ba zai goyi bayan wani abu da ya saɓa wa muradinsa ba, domin mu mutane ne masu riƙon amana, kuma za mu tabbatar da nasararsa a 2027,” in ji shi.

Saboda haka ya aika saƙo mai ƙarfi game da matsayar Arewa maso Yamma, yana mai bayyana kwarin gwiwar cewa yankin zai ci gaba da goyon bayan Tinubu yayin da zaɓen 2027 ke ƙaratowa.

Ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a siyasar ƙasar da su wuce tunanin muradun siyasa na ƙashin kai, su mayar da hankali kan haɗin kan ƙasa da ci gaban da zai amfani kowa.

By Babaji

Leave a Reply