Gwamnatin Gambia ta sanar da cewa za ta yi amfani da kuɗin da aka samu daga sayar da wani katafaren gida mallakar tsohon shugaban ƙasar, Yahya Jammeh, a Amurka domin biyan diyya ga mutanen da suka fuskanci take haƙƙin ɗan Adam a lokacin mulkinsa.
Hukumar biyan diyya ga waɗanda aka zalunta ta Gambia ta bayyana cewa ta karɓi dala 2,573,414.10 daga sayar da gidan da ke Potomac, Maryland, wani yanki da ke kusa da birnin Washington, DC.
An kwace kadarar ne bayan hukumomin Amurka sun ɗauki matakin shari’a kan zargin cewa an saye ta ne da kuɗaɗen da aka samu ta hanyar cin hanci da rashawa.
Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ta shigar da ƙara a shekarar 2020, yayin da kotu ta bayar da umarnin kwace kadarar a shekarar 2022.
Hukumar ta Gambia ta tabbatar da cewa an sanya kuɗin cikin asusun asusun biyan diyya da ke Babban Bankin ƙasar, tare da bayyana cewa za a yi amfani da su ne kawai wajen biyan waɗanda aka zalunta da kuma waɗanda suka tsira daga cin zarafin da ake dangantawa da mulkin Jammeh.
Yahya Jammeh ya mulki Gambia fiye da shekaru 22, kafin ya bar ƙasar a shekarar 2017 bayan ya sha kaye a zaɓen shugaban ƙasa na 2016. Ya ƙi amincewa da sakamakon zaɓen a lokacin, lamarin da ya haifar da rikici da matsin lamba daga ƙasashen yankin Afirka ta Yamma, har ya bar ƙasar zuwa gudun hijira a Eƙuatorial Guinea.
A lokacin mulkinsa, an zargi jami’an tsaro da aikata laifuka da suka haɗa da kame mutane ba bisa ƙa’ida ba, ɓatar da mutane, azabtarwa da kashe wasu daga cikin masu adawa da gwamnati. Wata hukumar bincike ta Gambia ta kiyasta cewa dakarun da ke ƙarƙashin mulkinsa sun kashe tsakanin mutum 240 zuwa 250.
Duk da cewa biyan diyya ba zai iya dawo da waɗanda aka kashe ko goge raɗaɗin da iyalansu suka sha ba, matakin na iya taimaka wa waɗanda suka tsira wajen sake gina rayuwarsu da kuma nuna cewa ana iya bin diddigin kadarorin da ake zargin an samu ta hanyar cin zarafin jama’a.
