Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
Kwamandan hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana cewa ba zai sake yi wa kowane ɗan siyasa yaƙin neman zaɓe ba, yana mai jaddada cewa shi ba ɗan siyasa ba ne.
Daurawa ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook da harshen Hausa a ranar Asabar, inda ya bayyana fatansa na ganin an samu shugabannin da za su yi adalci, su tausaya wa talakawa tare da kare haƙƙoƙinsu.
Furucin malamin ya zo ne bayan an saka sunansa tare da na tsohon shugaban hukumar kula da aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON), Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan, da wasu malaman addini cikin kwamitin ba da shawarwari kan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na gwamnan Kano na jam’iyyar APC.
Shugaban APC na jihar Kano, Hon. Umar Haruna Doguwa, ne ya fitar da jerin sunayen kwamitin, lamarin da ya jawo suka daga wasu masu sa ido kan harkokin siyasa da sauran jama’a, musamman game da shigar malaman addini cikin harkokin siyasa.
A cikin saƙonsa, Daurawa ya ce: “Ni ba ɗan siyasa ba ne, kuma ba zan yi wa kowa yaƙin neman zaɓe ba. Sai dai ina fatan Allah ya ba duk wanda zai tabbatar da adalci, ya tausaya wa talakawa, ya kare haƙƙoƙinsu tare da yin aiki don inganta rayuwarsu nasara.
“Allah ya ba mu shugabannin da suke masu gaskiya, riƙon amana da tsoronsa, waɗanda za su fifita muradun jama’a a kan muradunsu na kansu. Amin, ya rabbal alamin.”
Ko da yake Daurawa bai yi magana kai tsaye kan saka sunansa cikin kwamitin yaƙin neman zaɓen APC ba, furucinsa ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara kan rawar da malaman addini ya kamata su taka a harkokin siyasa gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
